Connect with us

LABARAI

Badakalar Miliyan 214: EFCC Ta Tasa Keyar Tsohon Kwamishinan Bauchi

Published

on


Hukumar yaki da cin hanci da kuma yakar masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zakon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon Kwamishinan Kudi na jihar Bauchi, Alhaji Garba Dahiru da wasu mutane uku bisa zarginsu da wawushe sama da naira miliyan dari biyu da sha hudu, da dubu dari bakwai da saba’in (214,770).

An gurnafar da sun din ne a gaban Mai Shari’a Muhammad Shitu na kotun Tarayya da ke da matsuguni a jihar Bauchi a jiya Alhamis.

Sauran wadanda EFCC ta gurfanar su ne Alhaji Halliru Abdullahi, Alhaji Saleh Hussaini Gamawa da kuma na karshensu Aminu Umar Gadiya kan tuhuma guda biyu. Na farko ana zarginsu da hada baki wajen amsar kudi ta barauniyar hanya, na biyu kuma ana tuhumar su da amsar kudin da ya wuce ka’ida a wani bangare na halasta kudaden haram.

Wannan kudin dai yana daga cikin naira miliyan dari biyar ne da aka amso a shekara ta 2015 a lokacin yakin neman zabe wanda aka amsa daga hanun Ministan albarkatun mai ta wancan lokacin Diezani Alison Madauke.

Dukkanin wadanda ake zargin sun ki amincewa kan sun ci wannan kudaden da EFCC ke tuhumarsu a kai.

Tun da farko, shari’ar wacce aka kasafta ta gida biyu, karar farko an shigar da Saleh Hussaini Gamawa da Aminu Umar Gadiya kan zargin wuwushe naira miliyan (142,4m), a yayin da kuma ake tuhuma ta biyu ga Garba Dahiru (tsohon kwamishinan kudi) da Hallihu Abdullahi wanda su kuma ake tuhumarsu da karkatar da miliyan 172,310,000.00 zuwa aljihunnsu.

Kotun dai ta bayar da su beli kan wasu sharuda masu tsauri kamar yadda lauyan da ke kare su ya roka.

Da yake zantawa da manema labaru bayan fitowa daga cikin kotun, Lauyan Hukumar EFCC Barista Abubakar Aliyu ya shaida cewar suna zargin wadan nan mutane hudun ne da amsar kudade fiye da kima, wanda hakan ya saba wa doka.

“Harka ce ta badakala da suka yi da kudaden kasa a lokacin zabe na 2015, wadannan kudaden da muke zargin wadannan mutane hudun, yana daga cikin tsabar kudi naira miliyan 500 da suka amsa suka kuma rarraba a tsakaninsu”

“Mun gurfanar da su, sun musanta, don haka ne muka nemi za mu gabatar da hujjojinmu a zama na gaba,”

Da yake bayanin dalilinsu na ware shari’ar da sauran wadanda suke zargi da alaka wajen cinye kudaden sai ya ce, “Mun ware shari’ar ne domin kowani mutum ya amsa abun da ya aikata a kan kowane lamari, don haka ne muka raba shari’un domin wani bangare ya ji da abun da ake tuhumarsa,” In ji Lauyan EFCC, Barista Abubakar Ali.

Haka shi ma, Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Barista Patirck Owoicho ya yi karin hasken cewa, “Ana tuhumarsu ne kan wasu kudade na kamfen din PDP da aka same su da su. Kudaden nan ba wai sun dauka ba ne, a’a ana tuhumarsu ne da cewar kudaden da suka taba din sun fi karfin abun da ya dace su taba. Kudin wai ya haura naira miliyan biyar da doka ta baiwa kowani dan kasa damar amsa,”

“Amma dukkanin wadanda na ke karewa sun musanta cewar basu aikata wannan laifin ba, don haka aka daga karar, ni kuma na gabatar da bukatar neman a bamu belinsu kuma a bisa tausayawar kotu ta ba mu belinsu,”

Baristan Patric ya bayyana cewar duk da cewar shadudan da kotu ta gindaya musu na belin sun so yin tsauri amma dole za su cika domin biyayya wa kotu.

Kotun dai a karkashin mai shari’a Muhammad Shitu ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 16 da 17 na watan Oktoban shekarar nan.

Kotun dai ta bayar da belinsu ne kan tsabar kudi ga kowannensu naira miliyan 50, hade da kawo mutune biyu-biyu da za su tsaya musu da kowanne ya kai matakin albashi na goma ko kuma wani mai mallakin gida ko fili a cikin garin Bauchi.

Kakakin hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa (EFCC) na shiyyar Arewa Maso Gabas, Bello Bajoga ya yi karin haske kan wannan karar “Mun gurfanar da su ne bisa zargin hadin baki da kokarin halasta dukiyar haram, muna zarginsu a shekara ta 2015 sun samu kudi naira miliyan 214,770. Daga cikin miliyan dari biyar na kudaden da aka amso daga hannun tsohuwar Ministar albarkatun Mai Madam Diezani Alison Madauke wanda kudaden sun samu asali daga wasu kamfanonin mai.

“Amfani da kudade sama da miliyan 5 ya saba wa doka, don haka ne muke tuhumarsu da amsar kudi ‘cash’ har wannan adadin wanda hakan saba wa doka ne”, in ji shi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai