Connect with us

LABARAI

Yawancin Matan Da Ake Kashewa, Mazansu Ke Kashe Su –Amina Mohammed

Published

on

Mataimakiyar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammed, ta ce a duk duniya, kusan duk 1 cikin 2 na matan da ake kashewa, tsaffin mazansu ne ke kashe su.

Malama Amina ta fadi hakan ne a Brussels wajen kaddamar da sabuwar hadaka a tsakanin Majalisar Dinkin duniya da kuma kungiyar Turai EU, ‘wani sabon makamin tadawa ‘yan mata da mata hankali, “abin da ya wuce.”

Da take yi wa kungiyar ci gaban Turai din jawabi,, cewa ta yi, ‘samar da dandamali na yin hadaka mai mahimmanci irin wannan, wani babban ginshiki ne na cimma manufar nan ta 5 na karfafa mata ta nan da shekarar 2030.

Ta ce, a wasu kasashen, wannan hadakar za ta fi mayar da hankali ne kan yawaitan rigingimun da ake haddasa wa mata.

“Sau da yawa, a irin wadannan kashe-kashen, mu kan taras da cewa matan sukan kai kuka ga ‘yan sanda ko kuma su nemi kulawa ta magani.

“Amma masu bayar da agajin ba su da cikakken bayanai ko kuma hanyar da za su gano hadarin hakan.”

Malama Amina, wacce take tsohuwar Ministan muhalli ce ta Nijeriya, ta ce, wasu daga cikin tashe-tashen hankulan da matan kan fuskanta suna faruwa ne sakamakon rashin cikakken tsaro da matan kan fuskanta, musamman ma a wuraren da matan ke neman hakkokinsu.

Ta yi nuni da siffar matan da ba a saka su a cikin duk wasu lamurra da suka shafi hukumce-hukumcen zamantakewa, an bar su cikin hadurran da ke cike da duniya, da suka shafi cin zarafin ‘yan mata da ma su matan kansu.

Yanzun da aka shiga cikin shekara ta uku, ta kaiwa ga manufar karni, (SDGs), kungiyar a shekarar 2018 ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da samar da daidaito a tsakanin jinsi.

“Ba tare da daidaito da kuma ci gaba ba, tabbas za mu ci gaba da zama ne a halin takaicin da muke cikinsa a yanzun, inda muke kokarin magance matsalolin duniya da rabin kadarar ta duniya kadai,: in ji ta.

Ta bayar da misali da bankin duniya, ta yanda ake son matan su yi daidaito da maza wajen ayyukan kwadagon da za su ci gajiyar dala triliyon 160 na jarukan samun ci gaba.

“Amma kuma a zahirance, yawan matan da ke cikin kumci da talauci ya zarta na maza sosai,” sannan kuma da kadan-kadan ne kawai ake samun hakan na canzawa.

Malama Amina, ta yi nuni da amfanin kaiwa ga manufar nan ta karni ga kasashe sama da 190 da suka sanya hannu kan wannan manufar, wacce take yin kira da tabbatar da samun daidaito da kuma karfafa mata.

Mataimakiyar babban Sakataren ta nuna gazawar majalisar wajen bayar da misali ta hanyar karfafa mata a cikin hukumominta.

Malama Amina ta ce, a karo na farko cikin tarihin Majalisar tana tafiya ne wajen karkatuwa ga daidaiton jinsi a cikin ma’aikatan manyan hukumomin ta da kuma wakilanta na musamman da take nadawa.

“Muna fa da sauran aiki babba a gabanmu. Sai dai mun shirya masa, muna kuma da zimmar aikata shi.” Mataimakiyar babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Muhammed, ta ce a duk duniya, kusan duk 1 cikin 2 na matan da ake kashewa, tsaffin mazansu ne ke kashe su.

Malama Amina ta fadi hakan ne a Brussels wajen kaddamar da sabuwar hadaka a tsakanin Majalisar Dinkin duniya da kuma kungiyar Turai EU, ‘wani sabon makamin tadawa ‘yan mata da mata hankali, “abin da ya wuce.”

Da take yi wa kungiyar ci gaban Turai din jawabi,, cewa ta yi, ‘samar da dandamali na yin hadaka mai mahimmanci irin wannan, wani babban ginshiki ne na cimma manufar nan ta 5 na karfafa mata ta nan da shekarar 2030.

Ta ce, a wasu kasashen, wannan hadakar za ta fi mayar da hankali ne kan yawaitan rigingimun da ake haddasa wa mata.

“Sau da yawa, a irin wadannan kashe-kashen, mu kan taras da cewa matan sukan kai kuka ga ‘yan sanda ko kuma su nemi kulawa ta magani.

“Amma masu bayar da agajin ba su da cikakken bayanai ko kuma hanyar da za su gano hadarin hakan.”

Malama Amina, wacce take tsohuwar Ministan muhalli ce ta Nijeriya, ta ce, wasu daga cikin tashe-tashen hankulan da matan kan fuskanta suna faruwa ne sakamakon rashin cikakken tsaro da matan kan fuskanta, musamman ma a wuraren da matan ke neman hakkokinsu.

Ta yi nuni da siffar matan da ba a saka su a cikin duk wasu lamurra da suka shafi hukumce-hukumcen zamantakewa, an bar su cikin hadurran da ke cike da duniya, da suka shafi cin zarafin ‘yan mata da ma su matan kansu.

Yanzun da aka shiga cikin shekara ta uku, ta kaiwa ga manufar karni, (SDGs), kungiyar a shekarar 2018 ta mayar da hankali ne wajen tabbatar da samar da daidaito a tsakanin jinsi.

“Ba tare da daidaito da kuma ci gaba ba, tabbas za mu ci gaba da zama ne a halin takaicin da muke cikinsa a yanzun, inda muke kokarin magance matsalolin duniya da rabin kadarar ta duniya kadai,: in ji ta.

Ta bayar da misali da bankin duniya, ta yanda ake son matan su yi daidaito da maza wajen ayyukan kwadagon da za su ci gajiyar dala triliyon 160 na jarukan samun ci gaba.

“Amma kuma a zahirance, yawan matan da ke cikin kumci da talauci ya zarta na maza sosai,” sannan kuma da kadan-kadan ne kawai ake samun hakan na canzawa.

Malama Amina, ta yi nuni da amfanin kaiwa ga manufar nan ta karni ga kasashe sama da 190 da suka sanya hannu kan wannan manufar, wacce take yin kira da tabbatar da samun daidaito da kuma karfafa mata.

Mataimakiyar babban Sakataren ta nuna gazawar majalisar wajen bayar da misali ta hanyar karfafa mata a cikin hukumominta.

Malama Amina ta ce, a karo na farko cikin tarihin Majalisar tana tafiya ne wajen karkatuwa ga daidaiton jinsi a cikin ma’aikatan manyan hukumomin ta da kuma wakilanta na musamman da take nadawa.

“Muna fa da sauran aiki babba a gabanmu. Sai dai mun shirya masa, muna kuma da zimmar aikata shi.”

Advertisement
Click to comment

labarai