Connect with us

LABARAI

Ya Zama Tilas Mu Samar Wa Da Matasa Dama –Osinbajo

Published

on


Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya yi imanin cewa, yana da mahimmanci ga kowace gwamnati ta samawa matasanta dama.

Farfesa Osinbajo, ya karfafa hakan ne cikin jawabinsa a ranar Talata wajen kaddamar cibiyar kula da matsayin al’umma ta sashen arewa maso gabas, a Yola, shalkwatar Jihar Adamawa.

Ya yi nuni da cewa, yana da mahimmanci ga ‘yan Nijeriya su yi tunanin wasu matsalolin da ke fuskantar kasarnan, su kuma yi tunanin hanyoyin magance su.

Mataimakin Shugaban kasan, ya ce, an kafa wannan cibiyar ne da nufin samar da wurin da ya dace da yin irin wannan tunanin.

“Ina son na shaida maku cewa ni kam na gamsu, don haka, ina da tabbacin hanya daya da za mu ciyar da kasarmu gaba, ita ce hanyar fasahar zamani,” ya fadi hakan ne cikin takardar jawabin da babban mataimakinsa kan harkokin manema labarai, Laolu Akande, ya fitar.

“Matasanmu da kuke gani a kullum, suna yin irin wadannan abubuwa masu bam mamaki, sune suke nuna makomar kasarrmu a nan gaba.

A nan sai Osinbajo ya ce, gwamnatin tarayya ta himmantu ne wajen yin aiki da ire-iren wadannan cibiyoyin a cikin shirye-shiryenta.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayyan tana da nufin kafa irin wadannan cibiyoyin guda shida a sassan kasarnan, ya kara da cewa, cikin nan da ‘yan makonni za su kafa wata makekiyar cibiyar binciken yanayi a Jami’ar Legas.

Mataimakin Shugaban kasan ya ce, sun fara yin wata gasa ta makarantun Jami’o’i da makarantun kimiyya da fasaha, wanda zai kunshi dalibai ne daga dukkanin sassan kasarnan.

Ya ce, “Baya ga wannan ma, za mu gina irin wadannan cibiyoyin guda shida cikin Jami’o’in kasan nan, masu nasaba da bincike a sassan kasarnan, farawan da muka yi da jami’ar Legas yana nuni ne da cewa har ma mun fara din.

Farfesa Osinbajo ya shaida wa mahalarta taron cewa, gwamnati ta hada wani kwamiti da ya kunshi matasa maza da mata, wanda zai taimaka wajen gyara tsarin kimiyya da kirkire-kirkire.

Sannan ya yi ma dukkanin wadanda suka taimaka wa gwamnati wajen samun nasarar kafa cibiyar binciken, musamman ma kungiyar Red Cross.

A nan ne take yanke, ya kaddamar da bude cibiyar binciken ta Arewa maso gabas, wacce za ta amfanar da al’umman yankin da ma Najeriya bakidaya.


Advertisement
Click to comment

labarai