Connect with us

LABARAI

Shugaba Buhari Ya Ja Hankalin Masu Son Zuba Jari A Nijeriya

Published

on


Shugaban kasa  Muhammadu Buhari ya sanar da cewa gwamnatin sa tana da abubuwan da za su janyo hankali wajen zuba jari a fannin yawon bude ido a kasar nan, musamman a kan manyan ayyuka da wuraren shakatawa.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin sa lokacin bude taro karo na 61 na majalisar dinkin duniya akan yawon shatawa da bude ido na hukumar Afrika.

A cewar sa, sauran fannonin sun hada da sufuri da samar da kayan aiki da inda ake cin abinci wanda ba’a Nijeriya aka sarra fa ba da saukaka haraji akan chacha da bayar da damar aiki ga ma’aikatan da za su shigo daga kasashen duniya wadanda suke kwararrun a fannin.

Shugaban wanda sakataren gwamnatin tarayya   Boss Mustapha ya wakilce shi a wurin taron yaci gaba da cewa, gwamnati a yanzu tana kara zurfafa shugabanci da samar da kariya akan yanci.

A cewar sa, shugabancin zai kuma tabbatar an samar da tsaro, musamman ga wadanda suke cikin fannin.

Buhari ya kara da cewa, “masu girma da manyan baki maza da mata, abin zai birge ku ganin cewar Nijeriya tana da alummar da suka kai sama da yawan    miliyan 180 da kuma sama da kabilu 250 da dukkan su suke tarihi daban-daban, inda wannan tarihin nasu akan yisu a fina-finai da kade-kade da kuma wake-wake don nishadantarwa.

Buhari ya yi nuni da cewar, wakoki da fina-finan mu sun baiwa duniya bazata  ganin yadda muke da yara masu hazaka a fannin, haka kuma sauran masu tasowa suna nan zuwa a nan gaba.

Shugaban ya ce, a bisa wadannan dalilan ne nake cewa masu son zuba jari a Nijeriya su dauki kasar a matsayin gidan su na biyu.

Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa, wannan gwamantin tana tana da wuraren da za a zuba jari kuma a shirye take wajen ma yabawa shugabancin   hukumar ta CAF da kuma ministocin ma’akatun yawon shakatawa da bude ido da suka fito daga kasashen Afrika a bisa zabar

Nijeriya a matsayin kasar data chanchici daukar nauyin taron na wannan shekarar.

Shi ma a nashi jawabin ministan ma’akatar yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya yi nuni da cewa, taken taron na wannan shekarar “ yawon shakatawa da bude ido hanyar samar da ci gaba” abu ne da yazo akan gaba, ganin yadda Nijeriya take kara samun ci gaba a fannin mayar da hankali na ba sai lallai an dogara akan mai da gas ba.

Lai Mohammed ya kara da cewa,  yawon shakatawa da bude ido fanni ne dake inganta tattalin arzikin kasa na sauran kasashe wakilai, musamman kuma abu mai mahimmanci dake taimakawa wajen samar da kudaden musaya na kasashen waje da aikin yi da samar da kudin shiga da karfafawa masana’antu gwiwa da kuma rage radadin talauci.

A cewar sa, yana daya daga cikin fannin da muka gano yana taimakawa wajen habaka tattalin arzikin kasa kuma fanni ne da zai tallafawa tattalin arzikin kasa na kasashe ‘yayan kungiyar.

Ya bayyana cewar taron ya samar da dama wajen tattauna hanyoyi inganta zirga-zirga da yawon bude ido.

A cewar sa, “Ina mai sa ran wannan taron zai zama shinfida wajen kafa hadaka a tsakanin wakilan kasashen don cimma burin da suka sanya a gaba.

A namu bangaren kasar mu tana yin iya kokarin ta cin ciyar da fannin yawon shakatawa da bude ido, inda don cimma wannan burin muka zuba jari da yawa a fannin.


Advertisement
Click to comment

labarai