Connect with us

LABARAI

Rashawa: EFCC Ta Gurfanar Da Mataimakin Shugaban PDP Na Kasa

Published

on


A Jiya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato (EFCC) ta gurfanar da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Babayo Garba Gamawa da wasu mutu ne biyar (5) a gaban kotun Tarayya da ke Bauchi a karkashin mai shari’a Muhammad Tukur kan zargin cin hanci da rashawa a kokarinsu na halasta kudin haram.

Kudaden da ake zarginsu sun amso daga hanun tsohowar Ministan Albarkatun Mai Diezani K. Alison-Madueke a shekara ta 2015 a lokacin da ake kokarin gudanar da babban zabe.

LEADERSHIP A Yau ta nakalto cewar mutane shidan sune, na farko Alhaji Babayo Garba Gamawa tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi (yanzu haka shine mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasar Nijeriya), sai na biyu Aminu Hammayo wanda tsohon Sakataren gwamnatin jihar Bauchi ne, Aliyu Abdullahi Jalam wanda shi kuma tsohon mai taimaka wa gwamnan jihar Bauchi ne, sai kuma Dahiru Madaki mamba ne a cikin kwamitin neman zaben tsohowar gwamnatin jihar, da kuma Alhaji Isah Sunusi sai na shida Ahmad Ibrahim Dan Dija tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi ne sune EFCC ta gurfanar da su kan lakume miliyan 500.

Wakilinmu ya labarto cewar muhawara mai karfi ta barke a tsakanin Lauyoyin EFCC da kuma na masu kariya a lokacin da kotun ke sauraro, hakan kuma ya faru ne a sakamakon rashin bayyanar wanda ake zargi na shida wato Ahmad Ibrahim Dan Dija a gaban kotun, inda masu karesa suka bayyana cewar bai da lafiya a yayin da kuma EFCC ta ki amincewa da hakan.

Wakilinmu ya shaida mana cewar hakan ya jawo zafafan muhawara daga bisani dai Alkalin Justice M. Shitu ya dakatar da su haka.

Lauyan Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zakon kasa EFCC Barista Abbakar Aliyu ya yi wa ‘yan jarida karin haske kan shari’ar da suka maka mutane shidan, inda ya bayyana cewar suna tuhumar mutane shidan ne da neman halasta kudin haram.

Ya ce, “Mun gurfanar da sune kan laifin kokarin halasta kudin haram, sun yi badakala naira miliyan dari biyar (500m) a shekara ta 2015 a lokacin da ake haba-haban yin zabe. suka karba hade da bayarwa, wanda a doka karbanta ma laifi ne, duk kudin da za a amsa a bi ta hanyar da ta dace, wannan shine muke zarginsu a kai,” In ji Lauyan EFCC.

Ya ce tuhumar da suke yi musu dai suna yi ne a kan hada-hada da kudaden ta barauniyar hanya, dangane da wanda ake zargi na shida da bai bayyana a gaban kotun ba, Lauyan ya shaida cewar idan bai zo ba za su nemi kotu ta kamosa a ko’ina yake.

Bayan fitowa daga kotun ne dai wakilan kafafen sadarwa suka tattauna da Lauyan daya daga cikin wadanda ake tuhuma da badakala na shida wato Barista Nasiru Balan Malam inda ya bayyana cewar wanda yake karewa wato Ahmad Ibrahim Dan Dija bai halarci kotun ba ne a sakamakon rashin lafiya da ta addabesa amma yana mai shaida cewar zai bayyana a gaban kotun a zaman da za a yi na gaba da yardar Allah.

Lauyan ya ce, “Abun da ya faru shine baya da lafiya, kuma rashin lafiya wani abu ne wanda daga Allah yake, dokokinmu sun kuma yarda kan cewar rashin lafiya yana daya daga cikin abun da zai sanya a baiwa mutum uzuri daga halartar kotu,” In ji Lauyan.

Ya kuma shaida cewar za su bayyana da shi da wanda yake karewa zuwa ranar da kotu ta ware “Insha Allahu ba mu da wani haufi kan halartar wanda na ke karewa amma abun da muke tsoro maganace muke yi ta rashin lafiya wanda ba a hanuna yake ba, ba a hanun kowa ba. amma indai a kan wannan tuhumar ne babu abun da zai hanasa zuwa in Allah ya yarda,”  cewar Lauyan.

Kakakin hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa (EFCC) na shiyyar Arewa Maso Gabas, Bello Bajoga ya yi karin haske kan wannan karar “Mun gurfanar da sune bisa zargin hadin baki da kokarin halasta dukiyar haram, muna zarginsu a shekara ta 2015 sun samu kudi naira miliyan dari biyar daga hanun Ministan albarkatun Mai Madam Diezani Alison Madauke wanda kudaden sun samu asali daga wasu kamfanonin mai.

“Wannan kudaden an karkatar da su aka raba wa ‘ya’yan wata jam’iyya a wancan lokacin, a cikin rabiyar ne aka turu wani kaso jihar Bauchi, su ‘ya’yan jam’iyyar a jihar Bauchi sai wasu suka wawushe,”

Jami’in hulda da jama’a ya kara da cewa “Mun yi bincike muna zarginsu, ita kotu ne za ta tabbatar suna da laifi ko basu da shi, amma mu muna da hujjojinsu da muka binciko,” A cewar Bello Bajoga.

Bayan dai tafka muhawara kan rashin halartar wanda ake zargi na shida a tsakanin Lauyoyi. Alkalin kotun Tarayya a jihar Bauchi Justice M. Shitu ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Satumba, 2018 domin ci gaba da sauraro hade da umurtan wanda bai hallara a gaban kotun ba da cewar ya hallara.

Sai dai kuma wakilinmu ya labarto cewar dukkanin shari’ar ta tsaya ne kan neman halartar wanda ake kara na shida da kuma rashin zuwansa


Advertisement
Click to comment

labarai