Connect with us

LABARAI

Osinbajo Ya Kaddamar Da Cibiyar Agaza Wa Jama’ar Arewa Maso Gabas A Yola

Published

on


Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da wata cibiyar da ofishinsa ya kirkiro domin agazawa jama’ar yankin arewa maso gabas NorthEast Humanitarian Innobation Hub, a Yola.

Da yake jawabi a taron mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yace gwamnatin tarayya zata kafa irin wakannan ci biyoyin a yankuna shida na siyasar kasar, domin kirkiro da hanyoyin sarrafa na’ura, da samar da sabuwar al’ada ga matasa.

Osinbajo ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya na shirin ta bada dama ga matasa a kasar, domin su nuna na su kwarewar ta fannin kere-kere, musamman ganin yadda suke da hazaka, saboda idan babu ilimin fasahar kere-kere a kasa yana da wuya a iya samun ci gaba.

Ya ce “kasa ba zataje ko’ina ba mutukar bamu da masu fasahar kere-kere, dole mu yi wani abu domin mu karfafa irin wannan kokarin da yaranmu sukayi” inji Osinbajo.

Ya ce cibiyon shida da gwamnatin tarayya zata kafa zai taimaka wajan karfafa matasan a tannin fasahar kere-kere, ya ce gwamnatin tarayyar  tana aikin ganin ta samar da magora ga matasan da suka amfani da Damar da suka samu

Ya ce “muna kuma da wani shirin tallafawa masana’antu a kasa bakikaya, da maida hankali ga kirkire-kiren da fasaha, da dukkanin nau’in fasahohin da mutanenmu suke bukata domin su ci gaba, ina da tabbacin da buke wannan cibiya da wannan duniya za ta taimakawa matasanmu a wannan yankin, su rike kansu” inji Osinbajo.

Shima da yake jawabi a taron mataimakin gwamnan jihar Adamawa Martin Babale, ya ce gwamnatin jihar na maraba da cibiyar domin amfanin matasa a jihar.

Cikin tawagar mataimakin shugaban kasar sun haka da ministan lafiya Farfesa Isaac Adewale, da ministan mata Aisha Alhassan, da ministan kasafi Udoh Udoma, ministan muhalli Zainab Ahmed, da kuma sanata mai wakiltar Adamawa ta arewa Binta Masi Garba, da sauransu.


Advertisement
Click to comment

labarai