Connect with us

LABARAI

MURIC Ta Ce A Fallasa Wadanda Suka Sace Dabinon Sadaka Daga Saudiyya

Published

on


Kungiya mai rajin kare hakkin musulmi ta “Muslim Rights Concern (MURIC)” ta yi tir da yadda gwamnatin Nijeriya ta kasa bayana wa tare da hukunta wadanda suka karkatar dabinon da kasar Saudi Arabia ta bayar sadaka domin a rarrabawa ga ‘yan gudun hijira da wasu manyan masalatai na kasar nan.

Bayan da rahoton karkatar da dabinon ya fito ne da kuma cewa, ana sayar da dabinon a kasuwannin Abuja da jihar Barno, gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamiti don gano tare da hukunta masu hannu a badakalar.

A makon daya gabata ne, kafar watsa labarai na PREMIUM TIMES tayi bayanin cewa, har yanzu gwamnatin Nijeriya bata bayyana wa ‘yan Nijeriya sakamakon rahoton binciken da aka yi ba duk da a halin yanzu ana shekara daya kenan da badakalar, har yanzu kuma babu wanda aka hukunta a kan karkatar da dabinon.

A martaninta a kan rahoton, ta sanarwar da shugaban ta Ishak Akintola ya sanya wa hannu, kungiyar MURIC, ta ce, labarin badakalar rarraba dabinon abin kunya ne.

”Hankalin kungiyar MURIC ya yi matukar tashi, musamman zargin rashin gaskiyan da aka samu wajen rarraba dabino ga ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na Barno, in har wannan zargin ya zaman gaskiya” sanarwar da kungiyar ta bayar da aka sanya wa hannu ranar Alhamis.

“Dole a bi diddigi tare da kammala binciken yadda ya kamata, wannan abin kunya ne, in har Nijeriya zata yi yekuwar neman taimako ga ‘yan gudun hijira amma wasu marasa imani zasu karkatar da taimakon da aka kawo daga kasashen waje, lalla wannan rashin imani ne tsagwaronsa”

“kungiyar MURIC na bukatar sanin sakamakon binciken da ma’aikatan harkokin waje ta gudanar. Boye sakamakon binciken nada matsala kwarai da gaske domin kasashe masu bayar da gudummawa zasu iya yi daridari wajen taumakawa suna kuma iya dauka cewa, gwamnatin Nijeriya da sauran hukumomin ksar nan ba abin a amince musu bane a nan gaba” inji sanarwar.


Advertisement
Click to comment

labarai