Connect with us

LABARAI

Mun Himmatu Domin Rage Yawaitar Mace-macen Yara A Bauchi, Inji Dakta Zuwaira

Published

on


addada aniyarta na inganta alkaluman rigakafin yau da kullum domin takaita yawaitar mace-macen ‘yara ‘yan kasa da shekaru biyar a fakin jihar.

Kwamishiniyar lafiya a jihar Bauchi Dakta Zuwaira Hassan Ibrahim ita ce ta shaida hakan a sa’ilin da yake jawabi a wajen buke taron kara wa juna sani na kwanaki uku domin tattara tsare-tsaren da aka fitar da wakanda aka yi waje guda domin inganta harkar lafiya a jihar.

Dakta Hassan ta nuna fatan cewa rigakafin na yau da kullum zai taimaka gaya wajen rage yawan mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar, haka kuma zai basu zarafin samun kiyon lafiya mai inganci hake da samar musu da koshin lafiya a kowani lokaci.

A cewarta, kiddigar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gudanar a shekarar da ta wuce, kiddigar na nuni da cewa jihar Bauchi ta samu kashi 39 a cikin 100 na yaran da suka samu wannan rigakafin, har-ila-yau, a wannan wata uku na farkon wannan shekarar jihar ta samu maki 47 a cikin 100 na yaran da suka samu wannan rigakafin, wanda hakan ke nuni da cewa akwai nasarori sosai da suke samu a wannan bigiren.

Ta bakinta “Abun da muke so mu ga an aiwatar shi ne mu ga mun samu raguwa ta fuskacin rashin lafiyar yara, mun kuma samu rage yawaita mutuwar yara kanana da kuma rage rashin lafiyar iyaye mata da kuma mace-macen su kansu iyayeyn a wajen haihuwa, kama daga lokacin da suke da ciki, ko wajen haihuwa ko kuma bayan haihuwarsu, muna fatan mu ga an samu raguwar irin wakannan matsalolin sosai a jihar nan,” In ji Kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi.

Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar Bauchi Famasis Adamu Ibrahim Gamawa ya ce makasin wannan horarwar shine domin a fitar da tsarin gudanar da aiki shine domin a bullo da wata hanya na sanya dukkanin aiyukan da ake gudanarwa a fannin kiwon lafiya domin samun nasarar cimma yarjejeniyar fahimta a tsakanin gwamnan jihar Bauchi da sauran kungiyoyin tallafa wa harkar lafiya suka rattaba wa hanu domin inganta lafiya.

Adamu Gamawa wanda ya bayyana cewar muddin ba a fitar da wannan tsarin gudanar da aikin ba, wannan yarjejeniyar da suka sanya wa hanu ba lallai ya kai ga nasara ba, sai ya nemi dukkanin masu ruwa da tsaki kan sha’anin da suka kara kaimi da azama domin tabbatar da nasarar shirin.

Ya ce; “Ya zamana dukkanin abubuwan da suka shafi kiwon lafiya a matakin farko an sanya su a cikin wannan ‘MO’u’ ba za kuma ka samu cimma abubuwan da aka sanya wa hanu domin amincewa ba sai ka samu abun da zai zama maka jadawali to shi wannan jadawalin da tsarin ne muke horo domin fitar da shi a wannan lokacin,” In ji shi.

Shi dai wannan horaswar da ake yi a halin yanzu zai kai ga fitar da tsari na musamman na gudanar da aiki a fannin kiwon lafiya a matakin farko na sauran watanni shida na wannan shekarar da kuma shekara mai zuwa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai