Connect with us

LABARAI

Kanmu A Hade Yake Fiye Da Tsammanin Okorocha, Inji Oyegun

Published

on


Shugaban jam’iyyar All Progressibe Congress (APC) Chief John Oyegun yayi watsi da maganar bita da kullin da aka ce ana yi  ma Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, inda yake cewa ‘’Ba wani abinda ke faruwa na batancbi da ake yi  ma shi gwamnan’’.

Gwamna Okorocha yana zargin cewar shi shugaban jam’iyyar na kasa, yana neman yayi ramuwar gaiya ce wadda tafi ita gaiyar zafi, akan rawar daya taka, na tabbatar da cewar su ‘yan kwamitin zartarwa na jam’iyyar basu samu damar cika burinsu na, a barsu su zarce da yin shugabancin jam’iyyar.

Da yake jawabi  a wani taron da ya kira na janyewa daga takara, shugabancin jam’iyyar a Abuja, shugaban jam’iyyar na kasa, yayi kira da Gwamnan cewar ya kara ita maganar da yayi,saboda ai zarar bunu ce, inda ya ce, ‘’An hade mai kai’’.

Chief Oyegun dai bai bada wani cikakken bayani ba lokacin da aka tambaye shi,ko zai wani karin bayani akan zargin da Gwamna Rochas Okorocha ya yi , na ana yi ma shi bita da kulli, sai ya bada amsar cewar shi bai san daliliun da yasa shi Gwamnan yake da yawan koarafi ba.

Ya  kara da cewar shi bai ga Gwamna Okorocha a matsayin  wani babban wanda da yake taka, ko kuma ya taka babbar rawa, akan al’amarin rashin amincear dasu ci gaba da shugabanciun jam’iyya, ‘’Ba na jinhar akwai wani dalilin da zai sa nayi wani dogon jawabi dangane da wancan al’amarin ba’.

‘’Koda yake dai har yanzu ana cikin wancan takin sakar,don haka bai kamata na baka amsa ba, amma kukma wani babbar al’amari shi ne, maganar gaskiya, ai ba shi kadai bane bai goyi bayan mu ci gaba da mulkin ba na shugabancin jam’iyyar, don haka kuma mi zai sa ya ce, ana yi ma shi makarkashiya.’’

‘’Idan kuka duba abubuwan da suke faruwa a jihar shi, ina ganin zaku iya samun gaskiyar lamarin da yake tafiya  ajihar daya ke shugabanta, akwai muryoyin da suke bukatar da ayi wani abu akan yadda ake tafiyar da ita jihar’’.

Bugu da kari da yake jawabi a wani taro na yi ma ‘yan jarida bayani, tsohon shugaban kwamitin shirya yadda za gudanar da  taron kasa, Sanata Benjamin Uwajumogu, shi ma ya caccaki Gwamnan, inda ya kara cewar  su ‘yan jam’iyyar APC wadanda suke sashen Gabas maso Kudu, suna jin kunyar irin maganganun  da yake yi.

Shima da yake bada ta shi gudunmawar Uwajumogu ya bayyana cewar ‘’Idana aka yi la’akari da kashi 95 na ‘yan asalin jihar Imo, da kuma sauran sassan Kudu maso gabas wadanda suke jam’iyyar APC, basu farinciki da irin abubuwan da suke faruwa, a jihar Imo a karkashin shugabancin Gwamnan jihar Imo Okorocha.’’

‘’Jihar Imo yanzu ta zama  tamkar jihar wadda take da matsaloli fiye da kowa, daukacin al’ummar sashen Kudu maso gabas, suna jin kunyar, cewar jiha guda daya wadda take karkashin jam’iyyar APC, ana mulkin jihar ne kamar yadda muka ga wani a shekaru masu yawa da suka wuce.

‘’Ba ni da wani zabi illa na nisantar da kaina daga waccan gwmnatin, ina mai farin ciki saboda yanzu, na ajiye aikin, watakila taron zaben shugabannin jam’iyyar na kasa , ya tafi kamar yadda kowa ke so’’.

‘’Ina da masaniyar cewar shi Gwamnan yana goyon bayan wasu mutane ‘yan Kudu maso gabas, saboda su tsaya takarar mukaman da aka kai su sashen Kudu maso gabas’’.

‘’Don haka ina da masaniyar cewar ba nine sakataren taron ba, ba wanda zai ga laifi na cewar ko na kawo cikas , ko kuma yin wani abu da shi sakamakon zaben wadanda za a zaba a matsayin shugabannin jam’iyyar APC na kasa.


Advertisement
Click to comment

labarai