Connect with us

LABARAI

Fyade: Majalisa Za Ta Bi Diddigin Rahoton Zargin Amnesty Ga sojoji

Published

on


A ranar Laraba ne majalisar dattijai ta yanke shawarar binciken rahoton da hukumar kare hakkin dan adam ta “Amnesty International” ta fitar inda ta zargi hukumomin tsaron kasar nan da musgunawa da kuma yin fyade ga matan dake sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Barno.

‘yan ,ajalisar sun amince da kafa kwamitin don yin nazari tare da bincikar dukan zarge zargen da akayi wa sojoji da sauran jami’an tsaro dake aiki a yankin Arewa maso Gabas.

Yanke wannan shawarar ta biyo bayan kudurin da Sanata Shehu Sani dan jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya ya mikawa majalisar, inda ya nuna rashin gamsuwarsa da martanin da gwanatin Nijeriya ta mayar a kan rahoton, saboda haka ya bukaci majalisar dattijai ta sake bude lamarin don a yi bincike na musamman.

“Mata da dama sun bayyana yadda sojoji da ‘yan kato da gora suke amfani dad a karfi da kuma barazana wajen yi musu fyade a kananan sansanonin ‘yan gudun hijira, haka kuma jami’an tsaron na amfani da halin yunwa da fatara da matan ke ciki wajen tilastasu zama ‘yan matansu, ta haka sais u yi ta jima’I dasu babu kakkautawa” inji rahoton da aka fitar a watan Mayu.

A martanin nasu, fadar shugaban kasa da rundunar ‘yan kato d agora “Cibilian Joint Task Force (CJTF)”, sun ce, rahoton ba shi da halasci saboda bai kunshi kwararan hujjojin da za a iya dogaro dasu ba don gudanar da bincike mai mahimmanci irin wannan.

A kudurin nasa, Sanata Sani ya ki amincewa da hujojjin da aka gabatar a kan rahoton, saboda haka ya bukaci ‘yan majalisar dattijan dasu yi kyakywan bincike a kan zarge zargen da ake yi wa jami’an tsaron Nijeriya game da batun fyade.

“Wannan rahoton na “Amnesty International” yana da karfi sosai domin ya kunshi sunaye da hotuna da wuraren da aka yi fyaden da kuma bayanan wadanda aka yi wa fyaden da wadanda aka azabtar da yunwa da kuma wadanda aka gallaza musu”

“bayan fitar rahoton, fadar shugaban kasa da rundunar tsaron Nijeriya ta yi watsi da rahoton ne kai tsaye, a matsayinmu na ‘yan majalisa muna da hakkin gudanar da bincike don yin maganin wannan lamarin” inji shi.

Ya kara da cewa, Nijeriya nada hakkin kallan rahoton yadda ya kamata kamar dai yadda ake daukan irin wannan rahoton da mahimmanci a wasu kasashen duniya.

“A matsayinmu na kasar dake a tafarkin dimokradiyya, muna na hakkin yaki da dukkan nau’in ta’addanci da kuma kare hakkin ‘yan Nijeriya a dukk inda suke a kuma kowanne lokaci.”

“Babban abin takaici shi ne, wannan rahoton bay a bata sunan rundunonin tsaron kasar nan kadai bane har ma da sunan kasar baki daya ya bata”

A nasa gudummawar, mataumakin jagoran majalisa, Sanata Bala Na’Allah, ya jawo hankalin ‘yan majakisar ne a kan irin wannan bincike da suke son yi saboda harkar yaki yana da tsananin sarkakiya.

Daga karshe dai ‘yan majalisar sun yanke shawarar kafa kwamiti mai karfi don binciken lamarin.


Advertisement
Click to comment

labarai