Connect with us

LABARAI

Daliban G4G Karkashin Kungiyar Unicef Sun Nuna Gamsuwa Da Taron Bita A Bauchi

Published

on


 

‘Yan mata daliban makarantun firamare da na karatun allo da kungiyar UNICEF tare da hadin guiwar kungiyar FAHIMTA  suka fara aikin ba su horon bita  kan samun ingancin shugabanci da dogaro da kai sun bayyana jin dadi game da yadda kungiyoyin suka nuna damuwa game da halin da suke ciki tare  gayyatar su don ilmantarwa game da yadda za su fahinci lamurran rayuwar yau da kullum.

Taron bitar wanda aka fara ranar litinin da ta gabata an gayyaci yara mata 100 daga kananan hukukumomin  Toro da Ningi da Zaki inda aka ajiye su a Otel din Zaranda domin basu bitar koyon sana’a da ilmin zamani da na addini da kuma hikimar shugabanci a gida da makamantan su. A saboda haka wakilin mu ya ziyarci wajen da ake horas da yaran, wadanda ke koyon ayyukan girke girke da yin kayan adon wuya na mata da jakkunan hannu da sauran kayan abinci da na kawata gida. Akasarin daliban sun bayyana cewa sun ji dadin shirya musu wannan bita kuma za su yi amfani da abin da suka koya idan sun koma garuruwan su don fara tarbiyyantar da kan su don samun ingancin rayuwa.

Wata Yarinya Rukayya Mohammed Auwal wacce ta zo daga makarantar firamare ta tudun wada a Toro ta bayyana cewa akwai kayayyakin da ta ke gani ana amfani da su wajen yin ado amma bata san yadda ake yin su ba amma yanzu ta fahimci aiki ne mai sauki yadda ake hadawa da kuma yadda ake sayen kayan da ake hada su. Don haka ta bayyana cewa ta yi mamaki game da yadda suka samu karin ilmi kan ayyuka masu yawa, ta bayyana cewa idan ta koma gida za ta ilmantar da kannen ta da abokai tare kuma da sayen kayan da ake hada wasu abubuwan don ta rika yi tana sayarwa a gida.

Hajiya Maryam Garba shugabar kungiyar FAHIMTA wacce ke jagorantar wannan taron bita ta bayyana cewa yara matan da ke amsar wannan horo suna da fahimta tare da nuna sha’awar su kana bin da ake karantar da su. Don haka ta bayyana cewa sun tsara yadda su ke koya musu sana’a yadda kowace yarinya za ta iya abin da aka koyar da wata gobe kuma sai a koyar da wasu, yayin da wani lokacin kuma sai koyar da su karatu na addini da na boko da darussa da dama. Ta ce duk da karancin lokaci da ake da shi amma yaran za su koyi abubuwa masu yawa da za su amfana tare da amfanar da ‘yan uwan su a gida.

Shi ma shugaban kungiyar UNICEF me lura da ofishin da ke shiyyar Bauchi Mista Bhanu Pathak wato Chief of Field ya ziyarci wurin taron bitar a wannan larabar yadda ya kara wa yaran karfin guiwa a kan abin da ake koyar da su, inda ya bayyana cewa su gode wa Allah da suka zo a wannan lokaci da rayuwa ke da sauki ake amfani da na’urorin zamani da suka kunshi wayoyi da na’urori masu kwakwalwa da suke taimakawa wajen koyon abubuwa cikin sauki  da ci gaba irin na zamani. Ya bayyana cewa a kasar su ya tashi ne a rayuwar kauye inda ya yi karatu a gindin bishiya kuma ya fiskanci kalubale da dama na rayuwa, amma yanzu bayan ya samu ilmi cikin wahala yana aikin da ya ke taimakon mutane a duniya.

Don haka cikin raha  Bhanu Pathak ya shawarci yaran su himmatu wajen sa zuciya a duk wata hidima ta ci gaba don su koya su amfanar da kansu da iyayen su saboda sune manyan gobe da iyaye da gwamnati za su yi amfani da su wajen samar da ci gaban kasa. Ya yaba game da himmar da ya ga yara matan suna nunawa wajen koyon abubuwan da ake koya musu, don haka ya bukace su da su kara himma su kasance masu ladabi da biyayya ga iyaye da shugabanni don su ci moriyar rayuwa, musamman ganin su kananan yarane da suka kama daga shekaru goma zuwa 15, don haka suna da lokaci mai yawa a gaban su da za su amfanar da kan su da wasu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai