Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Ayyana 12 Ga Yuni A Matsayin Ranar Dimokradiyya

Published

on


 

  • Ya Ba Abiola Lambar GCFR
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin cewa, daga wannan shekarar 2019, bukin ranar dimokradiyya da ake yi a ranar 29 ga watan Mayu da kowanne shekara tun shekara 18 da suka wuce, yanzu an mayar dashi zuwa ranar 12 ga watan Yuni domin karrama Cif Moshood Abiola, dan takarar jam’iyyar SPD daya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 1993.

Alkalummar zaben ya nuna cewa, Cifa Abiola ne ya lashe zaben amma a hukumance ba a aiyyana shi a matsayin wanda ya ci zaben ba kuma gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Ibrahim Babangida bai rantsar da shi ba.

Gwamnatin mulkin soja na Janar Sani Abacha ta garkame Cif Abiola a gidan yari bayan daya shiga gwagwarmayar neman hakkinsa, ya rasu a gidan yari a shekarar 1998.

Gwamnatocin da suka gabata sun kawar da kai daga kiraye kirayen da aka yi ta musu na a karrama Mista Abiola da kuma bukatar gwamnatin tarayya ta mayar da ranar 12 ga watan Yuni ranar dimokradiyya.

Gwamnatin Buhari ta ce, a halin yanzu za a karrama Mista Abiola da lamban girma mafi daraja da girma a kasar nan, lamba girman da aka ware wa shugaban kasa da tsaffin shugabannin kasa kawai, wato, “Grand Commander of the Federal Republic, GCFR”.

Gwamnati ta kuma ce, mataimakin Mista Abiola a zaben da aka gudanar, Ambasada Babagana Kingibe, za a karrama shi da lamban girmamawa na biyu a daraja a kasar nan wato “Grand Commander of the Niger, GCON.”

Wadanda za a kuma karrama da lamban GCON akwai dan rajin kare hakkin jama’a da mulkin dimokradiyya Cif Gani Fawehinmi SAN.

“A tsawon shekaru 18 da suka wuce, Nijeriya na bikin ranar dimokradiyya ne a ranar 29 ga watan Mayu, wannan ranar ce a karo na biyu da zababben gwamnatin farar hula ke karbar mulki daga hannu gwamnatin soja. Karo na farko ya faru ne ranar 21 ga watan Oktoba 1979. Amma a ra’ayin mafi yawan ‘yan Nijeriya da wannan gwamnatin manu ranar 12 ga watan Yuni yafi kasancewa da tasiri a kan fafutukar dimokradiyyarmu fiye da ranar 29 ga watan Mayu har ma ya fi ranar 1 ga watan Oktoba da muka samu ‘yancin kai.” Inji sanarwa data fito daga fadar shugaban kasa ranar Laraba.

“Ranar 12 ga watan Yuni 1993, rana ce da miliyoyin ‘yan Nijeriya suka fito suka bayyana ra’ayinsu a dimokradiyyance, rana ce da akayi zaben da ba a taba yin zabe mai tsafta irinsa ba a tarihin kasar nan tun da aka samu ‘yanci kai daga hannun turawa. Kasancewa gwamnatin soja na wanna lokacin sun ki fito da sakamakon zaben bai dakile haske da kwar jinin zaben ba da kuma tsaftar dake tattare da yanayin da aka yi zaben.

“Saboda haka, bayan cikakken tattaunawa, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cewa, daga yanzu ranar 12 ga watan Yuni zai zama ranar bukin dimokradiyya a kasar nan. Haka kuma gwamnati ta yanke shawarar karrama marigayi Cif MKO Abiola wanda aka tabbatar da  shi ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni 1993 da lamba mafi daraja da girma a kasar nan na GCFR, mataimakinsa Ambassador Baba Gana Kingibe kuma za a karrama shi da  lambar GCON. Haka kuma za a karrama Chief Gani Fawehinmi SAN da lamban GCON, za a yi bukin karramawar ne a ranar 12 ga watan yuni 2018, daga nan kuma nan gaba ranar zai zama hutu don bikin ranar dimokradiyya ta Nijeriya.


Advertisement
Click to comment

labarai