Connect with us

LABARAI

’Yan Fashi Sun Dabawa Dan Shekara 23 Wuka A Kebbi

Published

on


A jiya ne a wani kauyen Tungar Magaji da ke a karamar hukumar mulki ta KoKo-Besse ‘yan fashi suka daba wa wani dan acaba mai suna Kabiru Labaran dan shekaru 23 da haihuwa a duniya  yuka ga wuya da kuma ciki da kuma samun nasarar arce wa da mashi dinsa a jiyan.

A cewar wata majiya mai tushe ta ce “ daya daga cikin ‘yan fashin ne ya dauki Kabiru da cewa yayi masa acaba zuwa wani kauye a cikin kauyuyukan da ke kusa da Tungar Magaji bayan sun Kama hanyarsu ta zuwa kauyen sai dan fashin ya dabawa kabairu wuka ta bayan wuyansa da kuma ciki daga nan ya arce da mashin din kabiru Labaran”.

Daga nan Kabiru ya yi kuwwa domin neman agajin jama’ar gari, sai manoman da ke noma a gonakinsu da kuma jama’ar wasu kauyuyukan da ke kusa da wurin da abin ya faru sai suka karbe mashin din Kabiru daga hannun dan fashi din amma kuma dan fashi ya rance na Kare.

Ya ci gaba da cewa sun dauki Kabiru zuwa asibitin garin koko domin yamu agajin rayuwarsa daga likitotin asibitin ta koko.

Haka kuma daya daga cikin shuwagabannin garin Tungar Magaji malama Abdullahi Yusuf  ya bayyana wa manema labaru cewa “gaskiya ne dan fashi ya dabawa Kabiru Labaran yuka a bayan wuya da kuma ciki a yammacin jiya a kusa da wani kauyen Tungar Magaji da ke a karamar hukumar mulki ta KoKo-Besse”.

Haka kuma ya ce “mun taimaka ganin cewa Kabiru Labaran an kai shi asibitin garin koko domin samun lafiya,  kuma mun sanarwa jama’an tsaro faruwar lamarin kuma kafin zuwan su dan fashin ya arce daga hannun jama’ar da suka yi kokarin kama shi, maharan dai sun samu nasarar kwace mashin din Kabiru ga hannun dan fashin”.

Domin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ta kebbi LEADERSHIP A Yau ta samu kiran mai magana da yawun rundunar DSP Mustapha Suleiman” ya tabbatar da aukuwa lamarin inda ya ci gaba da cewa dan acaba Kabiru Labaran a kaishi asibiti kuma ya na cikin koshin lafiya”. Hakazalika kuma ya ce; “kafin jama’an rundunar su isa wurin da abin ya auku dan fashin ya rance na kare,  amma rundunar ta fantsama Fagen neman dan fashin da ya aikata laifin fashi da makami ga Kabiru Labaran”.

 


Advertisement
Click to comment

labarai