Connect with us

LABARAI

SUBEB Da Kungiyar Unicef Sun Ilmantar Da ‘Yan Mata 100 Karkashin Shirin G4G

Published

on


Kungiyar UNICEF mai tallafawa yara da mata a karkashin majalisar dinkin duniya tare da hadin guiwar hukumar lura da ilmi a matakin farko ta Jihar Bauchi wato SUBEB da kuma tallafawar kungiyar FAHIMTA mai rajin inganta rayuwar mata da matasa a Jihar Bauchi sun fara aikin ilmantar da yara ‘yan mata guda dari da aka zabo daga makarantun firamare da kuma makarantun alkur’ani don ilmantar da su sana’a da kuma ilmin tattalin rayuwa don samun ci gaba mai amfani.

Shirin wanda aka kaddamar da shi a Otel din Zaranda da ke Bauchi an fara ranar litinin zuwa asabat inda aka  zabo ‘yan mata kanana daga makarantun alkur’ani da makarantun firamare a kananan hukumomin Zaki mata 32 da Ningi 32 sai Toro inda aka dauko  36 saboda girmanta, kuma aka ajiye yaran a dakunan otal na Zaranda har zuwa ranar asabat da za kammala shirin tare da daukar dawainiyar yaran da basu abinci da tufafi da jakkuna da takalma don samun nasarar shirin.

Hajiya Maryam Garba shugabar kungiyar inganta rayuwar mata da matasa ta FAHIMTA cikin jawabinta ga manema labarai ta bayyana cewa kungiyar UNICEF ta dauki nauyin gudanar da shirin wajen bayar da kudi da masu koyarwa da motocin da aka kwaso yaran da kayayyakin da aka basu da wurin kwana da kuma matan da aka dauka don koyar da su da kuma lura da yaran tun daga dauko su har zuwa mayar da su ga iyayen.

Ta kara da cewa za a koyar da ‘yan matan karatu da ilmin zama da jama’a da lura da iyali da cikin gida tare da koyar da su sana’o’i da suka shafi dinki da saka da rini da kayan tsabtace gida irin su sabulu da omo da makamantan su da yin kayan sha dangin zobo da jinja da girke girke kala kala da yin jakkuna da kayan ado da kwalliyar mata da sauran su don ganin yaran sun samu ilmi game da tarbiyya da neman abin kai don su dogara da kan su saboda su ci ribar rayuwar su tun suna kanana.

Maryam Garba ta bayyana cewa shirin G4G wato Girls for Girls ya kafu karkashin UNICEF inda aka shiga yankunan kananan hukumomin Jihar Bauchi aka zabi wasu makarantun firamare da na addini aka kafa kungiyoyi kan wannan shiri na ilmantar da kananan ‘yan mata don ganin an basu tarbiyyar lura da karatu da kauracewa tallace tallace. Kuma a cikin kungiyoyin akwai shugabanni saboda haka yanzu aka dauko shugaba da sakataren kowace kungiya da masu lura da su aka kawo su Bauchi don samun wannan horo zuwa ranar asabat da za a mai da su gidajen su.

Hajiya maryam Garba ta kara da cewa akwai mutane 18 da aka dauko daga kananan hukumomi uku da su ka zo wannan bita don kula da yaran yadda kungiyar FAHIMTA ke lura da gudanar da shirin yayin da su kuma hukumar SUBEB ke tsarawa da bayar da umarni su kuma UNICEF suke daukar nauyin shirin ta hanyar bayar da kudi da kayan aiki. Bayan an kammala da wadannan kananan hukumomi kuma za a koma zuwa ga wasu kananan hukumomi da ake gudanar da wannan shiri a cikin su.

Bayan haka kuma duk dalibar da ta halarci shirin za a bata takardar shaida da sauran kayayyaki masu amfani don su ci gaba da bitar abin da suka koya saboda za su koma garuruwan su suma su hallara daliban da ke karkashin wannan shiri na G4G su rika karantar da su abin da suka koya yadda za a samu ci gaban manufar shirin wanda aka fito da shi don ilmantar da yara mata kanana tare da kawar da hankulan su daga tallace tallace da sauran hanyoyi marasa amfani.

 


Advertisement
Click to comment

labarai