Connect with us

LABARAI

Sojojin Nijeriya Sun Ceto Mata 58 Daga Hannun Boko Haram

Published

on


A ranar Litinin ne, rundunar Sojin Nijeriya ta ce ta ceto wasu mata 58 a garin Modu Kimeri, da ke Karamar hukumar Bama, ta Jihar Borno, da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka killace su a matsayin bayin da suke yin lalata da su. Rundunar Sojin kuma ta ce baccin su ta kuma ceto kananan yara 75 da kuma manyan mutane 15 daga hannun ‘yan ta’addan.

Mataimakin daraktan hulda da fararen hula na rundunar Sojin ta, ‘Operation Lafiya Dole,’ Onyema Nwachukwu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya saki a Maiduguri.

Kanar Nwachukwu, ya ce Sojojin runduna ta 21 tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na fararen hula ne suka ceto matan.

“A ranar Lahadi ne 3 ga watan Yuni, rundunar tamu ta ceto tsararrun, bayan wata fafatawa da nufin karkade yankin na Bama, Modu Kimeri da Gulumba Gana, daga guggubin ‘yan ta’addan da suke ta faman tserewa daga hare-haren da Sojojin namu ke ta kai masu a yankunan na tsibiran tafkin Cadi, da kuma kan iyakokin Jihar ta Borno.

“Tsararrun da muka ceto sun hada da maza majiya karfi 15, manyan mata 58 da kuma kananan yara 75. A lokacin da dakarun namu na hadin gwiwa suke bincikar manyan matayen, sun tabbatar masu da cewa, ‘yan ta’addan suna ajiye da su ne kawai a matsayin bayin da suke yin lalata da su,” in ji shi.

Ya kara da cewa, Budurwowi biyu ma daga matan suna dauke ne da juna biyu.

“Mutanan da aka ceton, sun ce hatta manyan mazajen cikinsu ba su tsira daga azabtarwan ‘yan ta’addan na Boko Haram ba, domin kuwa a kullum ayyuka masu wahala ake tilasta su yi.

“Rundunar Sojin dai ta ce za ta hannata mutanan da ta ceton a hannun jami’an kula da ‘yan gudun hijira na matsugununsu da ke Bama, don a duba su da kyau,” in ji shi.


Advertisement
Click to comment

labarai