Connect with us

LABARAI

Sheikh Gumi Ya Dirar Wa Salon Gwamnatin Buhari

Published

on


Shaharraren malamin addinin musuluncin nan na Kaduna, Shaikh Ahmad Gumi, ya kara fasa kwai a kan salon mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce, ba a yi wa ‘yan adawa bita da kulli ba a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Malamin addinin ya tayar da kura a kafafen sadarwa na intanet a makon jiya yayin da kalubalanci tozarcin da hukumar EFCC tayi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero, in da aka tursasa masa daukan allon dake nuna cewa, ya yi laifi.
Ya yi tsokacin ne a yayin gabatar da Tafsirin Alkura’ani mai girma ranar Litinin wannan makon. Malamin ya ce, tsohon mai ba shugaban kasa shawara a fafannin tsaro a lokacin mulkin Jonathan, Sanbo Dasuki, bai gallaza wa kowa ba, abin dake nuna cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck bai musgunawa kowa ba.
“Babu wanda zai iya nuna wani da Sambo Dasuki ya gallaza wa a lokacin mulkin Goodluck” “Amma a yau duk inda ka shiga kuka a keyi”
“Ta yaya ‘yan sanda zasu gaiyaci mutum mai mahimmanci kamar Shugaban Majalisar Dattijai? ai ‘yan sanda ne ya kamata su je su same shi saboda shi ne mutum na uku a tsarin mahimmanci a kasar nan..
“Bama son a rage mutuncin matsayin shugaban majalisar dattijai a idon mutane.
“Saboda kawai ana zargin mutum sai kawai a fara yanke masa hukunci? Daga zargi kawai?”
Daga nan ya kuma ce, Manzo Allah Muhammad (SAW) ya umurci jama’a dasu mutumta shugabanni a ciki a al’umma..
“Ya kamata a mutumta manyan mutane tare da basu girman daya kamata. In kuka wulakantasu kuna wulakanta kan kune, kuma in kun fadi zabe lallai za a yi muku irin abin da kuka yi wa wasu.
“Saboda haka dole gwamnati ta canza wannan halin, dole a daina tursasa wa ‘yan adawa da masu sukan gwamnati”
“Bata haka ake samun nasara ba, in kuna son yin nasara, ku tsayu a kan gaskiya kawai ku kuma fadi gaskiya a dukan lokutta. Na dade ina bayar da misali da kasashen Saudi Arabia da Egypt da Libya, abin daya sa suka gamu da fushin Allah kenan, muna adduar Allah ya kare mu daga fada wa cikin irin wannan halin” inji shi.


Advertisement
Click to comment

labarai