Connect with us

LABARAI

Iyaye Na Iya Gano ’Yan Kwaya A Cikin ’Ya’yansu –Dakta Dayyibah

Published

on


Ganin yadda matsalar shan miyagun kwayoyi ke kara ta’azzara a cikin al’umma, Kungiyar Jama’atud Da’awa bangaren mata ta shirya taron lacca tare da buda-baki ga matasa domin wayar musu da kai a kan masifar da ke tattare da shan miyagun kwayoyi.
Taron laccar wanda kungiyar ta saba gudanarwa duk shekara daga shekaru shidan da suka gabata, ya gudana ne a babban dakin taro na Makarantar Fu’ad Lababidi da ke shiyya ta uku a Unguwar Wuse da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da ta ke gabatar da lacca a kan hadurran jarabar shan miyagun kwayoyi, Kwararriyar Likitar da aka gayyata a wurin taron, Dakta Dayyabah Shaibu da ke aiki a Babban Asibitin Kasa da ke Abuja, ta yi bayanin cewa idan jarabar shan kwaya ta kama mutum, za ta janyo ma sa matsaloli a rayuwa ba ga bangaren kiwon lafiya ba har da sauran harkokin da suka shafi mu’amala da mutane.
“Illolin kamuwa da jarabar shan kwaya suna da yawa. Duk wanda ya kamu da jarabar shan kwaya ba zai fahimci karatun da ake koyar da shi a makaranta ba, zai rika batawa da mutane, abu kadan za a yi ma sa ya rika yin fadace-fadace da mutane, zai bata da kusan kowa a cikin zumunci sannan ya zama mara katabus a rayuwarsa”.
Likitar ta cigaba da bayanin cewa a sakamakon yadda wadanda jarabar shan kwayar ta kama suke amfani da hanyoyi daban-daban wajen boye abin da suke aikatawa, ya dace iyaye su mike haikan wajen daukan sababbin matakai na gano wadanda suke shan kwaya a cikin ‘ya’yansu.
“Wadanda jarabar shan kwaya ta kama suna amfani da dabaru daban-daban wajen hana mutane gane halin da suke ciki. Don haka wajibi ne iyaye su kara sanya ido da kula sosai a kan ‘ya’yansu. Za su iya zuwa wurin gwajin jini a auna yaran domin gano ko akwai wanda jarabar ta kama shi. Za a yi gwajin tamkar yadda ake yi wurin gano halittar jiki da ajin jinin da mutum yake da shi da sauran su. Likitoci za su iya gano mutum yana sha ko ba ya sha domin jinin zai nuna”, in ji ta.
Dakta Dayyabah ta kuma ce kokarin dakile wannan mugun alkaba’in na shan kwayoyi a tsakanin matasa bai kamata a bar wa iyaye su kadai ba, inda ta kara da cewa “kowa yana da rawar da zai taika wajen taimakawa a yaki shan miyagun kwayoyi a cikin al’umma ba wai sai iyaye ba kawai. Idan kana tare da dan’uwanka ko ‘yar’uwanka sai ka ga hali da dabi’unsa sun sauya, ba ya ma ka magana kamar yadda kuka saba yi ko yana kokarin janye jikinsa daga wani abu da kuka saba yi tare a gida, kar ka tsaya wata-wata, ka yi maza ka fada wa iyaye abin da ke faruwa domin a dauki mataki da wuri”.
Likitar ta hori iyaye su kara himma wurin sanya ido a kan kai-komon ‘ya’yansu wanda ta ce ta hakan ne za su samu cikakkiyar masaniyar halin da ‘ya’yan nasu suke ciki.
Da take karin haske kan taron laccar, shugabar reshen mata na kungiyar Jama’atud Da’awa da ta shirya taron, Amira Rakiya Bamalli, ta ce taron na bana shi ne karo na shida da suke shiryawa domin matasa kawai.
“Mukan tsaya ne mu yi nazarin wadanne irin matsaloli ne suke barazana ga tarbiyyar ‘ya’yanmu matasa sai mu zabi daya daga ciki mu shirya taron wayar musu da kai a kan yadda za su nisanci matsalar. Matasa ‘ya’yanmu maza da mata muke tarawa a yi musu lacca a karkashin shiri na musamman da muke da shi domin matasa mai suna ‘Jadafiya’. Yara daga shekara 11 da haihuwa zuwa sama muke gayyata.
“A bana mun zabi mu yi magana a kan shan miyagun kwayoyi ne domin fadakar da matasan a kan hadurran da ke tattare da hakan. Wadanda suka riga suka kamu da sha a wayar musu da kai su bari, sannan wadanda ba su kamu ba a karfafa musu gwiwa su kara nisantar abin”, a ta bakinta.
Amira Bamalli ta ce a bara an yi taron laccar ne a kan rashin amfani da intanet a kan ka’ida da matasa ke yi wadda ke sa su hana idonsu barci suna dube-duben shafukan da ba su kamata ba da sauran sharholiya, kana ta yi fatan mahalarta taron da sauran matasa na ko ina za su dauki darasin laccar su yi amfani da shi.
Daga bisani an kamala laccar tare da cin abincin buda-baki a dakin taron wanda ya samu halartar matasa da dama daga ciki da wajen Babban Birnin Tarayya Abuja.


Advertisement
Click to comment

labarai