Connect with us

LABARAI

FOMWAN Ta Raba Kayan Sallah Ga Wadanda Suka Musulunta

Published

on


Kamar yadda kungiyar mata musulmi ta FOMWAN ta jihar Kano, ta saba raba kayan sallah ga marayu da iyayen marayu tare da marasa galihu a duk watan azumin Ramadan duk shekara.

A wannan azumin da muke ciki ma kungiyar ta raba irin wadanna kayyakin ga al’ummar da suka rungumi addinin musulunci dake garin Gyalan a karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano, kamar yadda shugabar kugiyar Malama Sa’adatu Hashim ta shaidawa manema labarai jim kadan da dawowarsu daga garin na Gyalan .

Amirian kungiyar ta ce, kayayyakin da aka raba adinke suke sai dai sawa kwai a lokacin shagulgulan karamar sallar. Wadanda suka amfana sun hada da maza da mata harma da manya. Wani abu sabo da kungiyar ta fito da shi a lokacin rabon tallafin na bana shi ne hatta wadanda ba su shigo musuluncin ba an raba musu kayan, ta ce, sun yi wannan ne domin a kwadaitar dasu domin wata rana suma su shigo addinin na musulunci

Ta kara da cewa, hakika sun nuna farin cikin su sosai da wannan kulawa da kungiyar ta yi musu musamman wadanda a musulmai ba.

Hajiya Sa’adatu Hashim, ta ce, ko kafin wannan kungiyar ta FOMWAN ta dauki ragamar gina masu gini guda biyu na makaranta domin koyar da su sanin ilimin addinin musulunci da na zamani. Abin sha’awa har wasu daga cikin su sun samar masu da karin fili domin fadada ginin dakunan karatun da kuma gina bandakuna, ta ce, da zaran kungiyar ta kammala ginin za ta dauki nauyin malama wanda za ta je can domin koyar da su ilimin addinin musulunci da na zamani, sune kuma za su biya ta albashi.

Daga nan sai ta yi kira ga masu hali dasu kara himma wajen taimakawa addinin musulunci musamman samar musu da makarantu da kuma tallafawa wadanda suka musulunta da ma wadanda basu musulunta ba .

Shugabar ta yi amfani da wannan dama na kira ga wadanda suka shigo addinin musulunci dasu tabbatar sun shigo ne tsakani ga Allah da kuma tsoron Allah da kyautata mu’amala da yan’uwan su wadanda ba su rungumi addinin musulunci ba .

Daga karshe ta ce kungiyar ta FOMWAN zata ci gaba da fadakar da mata a kan abin da ya shafi koyarwar addinin musulunci da koya musu sana’oi daban-daban a ciki da unguwannin jihar Kano tare da kananan hukumomin jihar 44. Babu shakka a cewar Malama Sa’adatu Hashim, mata musamman na yankunan karkara na bukatar agajin al’umma da gaggawa wajen fadakar dasu ilimin addinin musulunci da koya masu sana’oin dogaro da kai.

 


Advertisement
Click to comment

labarai