Connect with us

LABARAI

Fasa Kurkukun Minna:  Ban Sa Hannu Kan Takardar Kashe Wani Mai Laifi Ba –Gwamna Bello

Published

on


Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja, ya musanta zargin cewa, harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a ranar Lahadi da dare a gidan Kurkukun Minna, aiki ne na wasu masu laifin da aka yanke wa hukuncin kisa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton da ke cewa, wani jami’in gidan Kurkukun da kuma wani mahayin babur, sun rasa rayukansu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari gidan Kurkukun, inda suka saki fursunoni 210.

Hakanan gwamnan ya karyata zargin cewa ‘yan kungiyar ta’addancin Boko Haram ne suka kai harin ko kuma ‘yan fashi da makami ne suka zo su saki ‘yan’uwansu da ke gidan yarin.

Gwamnan ya bayyana cewa, tun hawansa kujerar ta gwamna a shekarar 2015, bai sanya hannu kan wata takardar kashe wani mai laifi ba tukunna.

Gwamnan ya bayyana harin da cewa abin takaici ne, ya ce, gwamnatin Jihar za ta hada hannu da gwamnatin tarayya domin fuskantar matsalolin kayan aiki da na karancin jami’an tsaro a Kurkukun.

Ya kuma bukaci ma’aikatan Kurkukun da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wani taraddudi ba domin ana ci gaba da binciken musabbabin kai harin.

“Mu a nan Jiha, za mu duba matsalolin kayan aiki da na karancin jami’ai a gidan Kurkukun, amma dai kuma ya kamata mutane su kula da aikinsu yanda ya kamata.

Shi ma babban Kwanturolan gidajen Yarin kasarnan, Ahmed Ja’afaru, ya ce, ba wani dan Boko Haram din da ke gidan yarin na Minna.

Ya ce, bincike ne zai tabbatar da dalilin kai harin da kuma yadda ‘yan fursunan suka sami hanyar fita daga Kurkukun.

Sai dai, wani da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna, Malam Mohammed Umaru, ya ce, maharan sun iso gidan yarin ne cikin motoci hudu.

Ya ce, ‘yan bindigar suna isa sai suka raba kansu kungiya-kungiya, suka kuma umurci duk mazauna unguwar da kowa ya shiga gida sannan ne suka fara farmatan Kurkukun.

“Sun ce mana mu shiga gidajenmu, ba sa son ganin kowa a waje. Hakan ya sanya muka yi ta kiran ‘yan’uwanmu da ke waje muna ce masu kar su dawo gida har sai maharan sun tafi.

“Sun kashe wani jami’in gidan yarin guda wanda ya zo yin aikinsa na dare kenan da kuma mai babur din da ya kawo shi, In ji shi.


Advertisement
Click to comment

labarai