Connect with us

LABARAI

APC Za Ta Mulki Nijeriya Har Abada –Maman Taraba

Published

on


Ministar harkokin mata, Aisha Alhasan, ta bayyana fatanta na cewa, tana sa ran Jam’iyyar APC ce za ta mulki Nijeriya har abada.

Ta fadi hakan ne ranar Litini a Abuja, jim kadan da ta rantsar da shugabannin wani bangare na Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Taraba. Jam’iyyar ta APC dai a Jihar ta Taraba, kamar ta sauran Jihohi ne, wanda duk rigingimu ya addabe su.

Ministar, wacce ta nu na aniyarta na yin takarar Gwamna a Jihar ta Taraba, wacce ta fadi a zaben 2015, ta kara da cewa, ba a tarraya ne kadai Jam’iyyar ta APC za ta yi nasara ba, za ma ta sami nasara a wasu Jihohin da ba su a hannunta a halin yanzun.

Ta kuma ce, lami lafiya ne Jam’iyyar ta su ta APC za ta gudanar da babban taronta na kasa.

“Ai daman babban Jam’iyya kamar tamu ta APC ta gaji ‘yan kananan rigingimu kamar haka, amma da zaran mun kammala babban taron mu na kasa, za mu dawo ne bakidayanmu mu fuskanci Jam’iyyar da ke adawa da mu ta PDP, ina kuma tabbatar maku, APC za ta ci nasara a Jihohin da ma ba mu da su a halin yanzun a zaben na 2019, kamar ta nan Jihar Taraba.

“Zan tabbatar da na bi diddigi a sahen da na fito, kuma da yardar Allah Jihohin Gombe da Taraba duk na APC ne a 2019. Kar ma ku yi maganan Nijeriya, domin daman ta APC ce, ita din ce kuma za ta ci gaba da mulkan ta har abada.”

Ta ce, ta ci zaben gwamna a Jihar a shekarar 2015, kaddara ce dai ta hana ta zama gwamna.

Da take magana kan rabuwar da Jam’iyyar ta APC ta yi a Jihar ta Taraba, cewa ta yi, “Ina da hakkin zaban wanda ya kamata ya zama Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Taraba. Ba wata rabuwa da aka yi a Taraba. Duk kanmu a hade yake, ba wani sabani, sam bamu rabu ba. Siyasa ce kawai.

A watannin baya ne kadan, ‘Yar siyasar mai yawan surutu ta ce za ta goyi bayan tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben 2019, ko da kuwa Shugaba Buhari ya zartar da shawarar sake tsayawa takara. Inda ta bayyana Atikun da cewa shi, ubangidanta ne na siyasa.

Daga baya ne, kwamitin amintattu na Jam’iyyar ta APC ya neme ta da ta zo ta yi masa karin bayani a kan matsayin nata.

A ranar 14 ne ga watan Janairu, ta karyata jita-jitar da ke cewa tana shirin ficewa daga Jam’iyyar ta APC.

Daga nan kuma ta sake jaddada biyayyarta ga Shugaba Buhari, ta ma kara da cewa, “Ina nan daram a cikin Jam’iyyar ta APC, zan kuma ci gaba da zama a cikinta.”

 


Advertisement
Click to comment

labarai