Connect with us

LABARAI

An Bukaci Al’ummar Musulmi Da Su Kiyaye Harshensu

Published

on


An yi kira ga al’umman Musulmi da su guji yada labaran kanzon kurege da kuma furta kalaman kiyayya da za su iya haddasa rudani a cikin al’umma.

Dakta Abdullahi Nasir na babban asibitin Isanlu dake Jihar Kogi ne yayi kiran a kasidar daya gabatar a wajen laccar Ramadan da hukumar talabishan ta kasa (NTA) dake Lakwaja ya shirya a lakwaja, babban birnin jihar kogi a ranar Lahadin da ta gabata.

Dakta Nasir ya ce akwai bukatar ganin al’ummar musulmi sun kiyaye irin labaran da kalaman da suke furtawa, inda har ma ya kawo wasu surori daga cikin Alkur’ani mai tsarki da hadisai wadanda suka nuna illolin yada labaran karya da kuma kalaman kiyayya.

Ya ce Allah ya la, anci masu irin wadannan halaye ganin cewa halaye ne daka iya hura wutan rikici a cikin al’umma. Har ila yau ya bukaci al’ummar musulmi dasu kasance ja gaba wajen tabbatar da zaman lafiya.

Dakta Abdullahi Nasir wanda ya gabatar da lacca mai taken “Labaran Karya da kalaman kiyayya ta fuskar Islama (false News and Hate Speech-Islamic persectibe) ya ce Allah ya ce umurci musulmi dasu kasance sun zama masu bada shaida na gaskiya tare da fadin gaskiyar lamarin da idanunsu suka gani tare da kuma kaucewa nuna ta hanyar fadin gaskiya, inda ya kara da cewa abubuwa hudu da suke haddasa kalaman kiyayya sun hada da nuna tsattsauran ra, ayin addini da rigima ko rashin jituwa tsakanin shugabanni da mabiyansu da nuna bambancin yare ko launin fata da kuma tsananin kishi.A don haka yayi kira ga al’ummar musulmi dasu zama tsintsiya madaurinki daya domin ciyar da addinin musulmi gaba.

Kazalika ya bukaci musulmi dasu kasance masu biyayya ga shugabanni da Allah ya dora su a matsayin jagoransu.

Sai dai kuma a bangare guda, Dakta Nasir ya hori shugabanni dasu zama masu adalci da tausayi ga mabiyansu, yana mai jaddada cewa Allah ne ya zabe su dasu jagoranci al’umma, sannan ya tunatar da shugabannin cewa a ranan tashin alkiyama kowani shugaba zai bada bahasin yadda ya shugabanci al’ummarsa a gaban Allah (SWT). A nasa jawabin maraba, shugaban gidan talabishan ta kasa (NTA) dake lakwaja, Alhaji Yusuf Kailani ya ce sun zabo taken laccan ne domin wayarwa da jama, a kai tare ilimantar da al’ummar Musulmi game da batutuwar dake janyo muhawwara mai zafi a wannan lokaci da muke ciki, inda ya kara da cewa sanin kowane cewa labaran kanzon kurege da kuma furta kalaman kiyayya suna haifar da rashin zaman lafiya da tashin hankali a cikin al’umma.

Alhaji kailani ya kuma godewa Allah yada basu daman tattaro kan musulmi karkashin lema guda domin yin nazarin rawar da suke takawa a marsayin masu gyara halayen al’umma da kuma musulmi manyan gobe.

Daga nan ya godewa dukkan al’ummar musulmi da suka samu daman halartan bikin.

Shugaban bikin, mai Shari’a Nasir Ajana wanda kuma shine alkalin alkalan Jihar Kogi, ya yabawa al’ummar musulmi dake a gidan talabishan ta NTA lokoja a bisa shirya gagarumin lacca kana yayi kira ga musulmi dasu kasance abin misali wajen gudanar da al, amuransu na yau da kullum kamar yadda Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya koyar.

Ya kuma shawarci musulmi dasu rika gaskata labaru kafin su karar tare da kaucewa furta kalaman daka iya haddasa fitina a cikin al’umma.

Mai Shari’a Ajana ya ce duk da cewa a akwai yancin fadin albarkacin baki, akwai bukatar ganin jama, a sun bambantatsakanin yancin fadin albarkacin bakin da kuma kalaman kiyayya. Cikin mashahuran mutanen da suka halarci taron har da Mai Martaba Ohinoyi na Kasar Ebira, Alhaji Ado Ibrahim da Ejeh na Dekina, Dakta Usman Obaje da Sarkin Kwatan Karfe, Alhaji Abdulrazak Isah Koto da kuma Mai Martaba Sarkin lakwaja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi Na Uku.

Sauran sun hada da alkalin alkalai na Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajana da alkalin kotun addinin musulunci na jihar kogi, Mai Shari’a Zakariya Idakwoji da kwamishinan yan sandan jihar kogi, Alhaji Ali Aji Janga da wakilin gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ,Alhaji Abdulmumin Okara da kantomomin riko na kananan hukumomin lakwaja, Okene, Kotonkrfe da kuma mambobin kungiyoyin addini irinsu JNI da Council Of Ulama, u da kuma FOMWAN da dai sauran al’ummar musulmi. Wannan shine karo na biyu da hukumar ta NTA lakwaja ke shirya laccar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai