Connect with us

LABARAI

Za Mu Ci Gaba Da Ba Gwamna Ganduje Goyon Baya –Kwamared Ali

Published

on


Al’ummar jihar Kano suna anfana sosai daga irin salon Gwamnatin jihar kano da Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje yake jagoranta wajen bunkasa ci gaban jihar.

Shugaban karamar hukumar Dala, Kwamred Ali Ibrahim Yan’tandu ya bayyana haka da yake tsokaci kan zagayowar rana damakwaradiyya.

Ya ce ko wane fanni na rayuwa Gwamnatin Khadimul Islam  tana kokarin ganin ta kawo masa dauki dan bunkasa shi,kama daga harkar lafiya,hanyoyi ilimi da kyautata jin dadin jama’a.

Kwamred Ali Ibrahim Yan’tandu ya ce wannan kokari na Gwamna Ganduje a bayyane yake saboda ya karade ko’ina a jihar kano,akwai ayyuka da ake na lungu kal-kal da karkara salamu Alaikum wanda ake dada kawata kananan hukumomin cikin Birni tayi musu ayyukan magudanan ruwa da kuma sanya tayil da hakan ke kawata unguwanni da tsaftace su.

Ali Yan’tandu ya ce akwai manyan ayyuka da Gwamna Ganduje yayi na manyan hanyoyi na kasa da gadoji, akwai katafariyar hanyar kasa data sama da akayi a kofar ruwa dake yankinsu ta Dala wacce ba irinta a duk fadin kasarnan sannan kuma ta taimaka wajen rage cunkoso da ake samu a wajen a baya.

Shugaban na karamar hukumar Dala ya ce gata shatale-talen Dangi da ake  da kuma ta sabon titin fanshekara da akayi wannan duk yana daga cikin irin tagomashin zabar Gwamna Ganduje da akayi  ake kuma sharbar romon damakwaradiyya.

Ya ce wannan irin kyakkyawar jagoranci da Gwamnatin Kano take cikin shekaru uku tayi ayyuka da dama to ya zama wajibi ga duk mai kyakkyawan tunani da son ci gaban jihar kano da al’ummarta ya ci gaba da mara mata baya dayi mata addu’a ta fatan samun nasara dan dorawa ta sake zabarta a karo na biyu.

Kwamred Ali Ibrahim Yan’tandu ya ce al’ummar karamar hukumar Dala zasu ci gaba da baiwa Gwamna Ganduje hadin kai da goyon baya dan kaiwa ga nasara a zabe mai zuwa dan ci gaba da ayyukanda zasu anfani al’ummar jihar kano.

Ali Yan’tandu yayi kira ga al’ummar jihar kano kwata su tsaya su dubi irin kwao da kishin ci gaba da Gwamna Ganduje ya kawo su ci gaba da mara masa baya ta sake zabarsa a zabe mai zuwa .


Advertisement
Click to comment

labarai