Connect with us

LABARAI

’Yan Sanda Za Su Fara Fatattakar Haramtattun ’Yan Achaba A Legas

Published

on


Rundunar ‘yan sandan jihar Legs sun sanar da cewa, daga ranar 15 ga watan Yuni 2018 za su fara kama ‘yan acabar da aka haramta aiyukansu a fadin jihar Legas.

Shawarar haka ya fito ne bayan taron da aka gudanar tsakanin rundunar ‘yan sandan jihar Legas da kungiyar ‘yan achaba ta jihar tare da kwamishinan ‘yan sandan jhar Mista Edgal Imohimi, sakamakon harin da aka kai ofishin ‘yan sanda na Ibeshe inda aka kona motar ‘yan sanda ranar 30 ga watan Mayu 2018.

Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chike Oti, a sanarwar daya fitar, ya ce, taron ya samu halartar shugabannin kungiyoyin ‘yan achaba kamar su “Motorcycle Operators Association of Lagos State” da “Nagari Motorcycle Owners and Riders Association” da kuma kungiyar “Okada Riders Welfare Association.”

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa, “A yayin gabatar da taron, Kwamishinan ‘yan sanda, ya ce, ‘yan sanda zasu kama ‘yan achaba masu tayar da hankali tare dactabbatarbda an hukunta su yadda ya kamata”

Mista Oti ya kara da cewa, daga ranar 15 ga watan Yuni duk mashin da bashi da lamba da sauran takardu za a kwace shi, an kuma haramta wa bin manyan hanyoyi da manyan gada a fadin jhar.

 


Advertisement
Click to comment

labarai