Connect with us

LABARAI

Sakacin Iyaye Na Daga Cikin Tabarbarewar Matasa A Kasar Nan –Nata’ala

Published

on


An nemi Iyaye da su tsaye haikan wajen sauke nauyin da ke kansu ta fuskar tarbiya a kasar nan. Sarkin Hausawan Paiko, Alhaji Rabi’u Nata’ala ne ya yi kiran a lokacin da yake shagube kan muhimmancin watan ramalan ga manema labarai a minna.

Sarkin ya cigaba da cewar komai a kasar nan mun dogara ga gwamnati ne wanda wannan babban kuskure ne, gwamnati na iya bakin kokarinta domin dambu ne yai yawa ba ya jin mai, akwai bukatar mu iyaye da al’umma mu tashi tsaye dan kare al’adun mu. Yau fitsara tayi yawa a tsakanin matasan mu, barin wadannan kyawawan al’adun da muka gada yasa muka zama ba ma iya tunanin komai sai gwamnati tayi mana, dubi irin shigar ‘yayan mu a yau duk mai hankali yasan bai dace ba musamman ga ‘yayan mu mata kuma iyaye na kallo wannan ma sai gwamnati tace mana bai dace ba ne sannan zamu gyara, ka ga wannan kuskure ne babba ai.

Duk abu mai kyau yana cikin mutunci domin mutunta shi ake, bai da ce mu bar ‘yayan mu suna shigar da ta sabawa al’adun mu da addinin mu ba, yau dukkanin addinan guda biyu musulunci da na kirista ba sa na’am da wannan muguwar shiga ta ‘yayayen mu domin ya sabawa hankali wanda ne ke haddasa karuwar alfasha a cikin ‘yayan mu.

Da zaran ka duba mafi yawa abinda ke kawo yawaitan fyade ga ‘yaya mata yana da nasaba ne da irin suturun da suke sanyawa, ba sai mun jira gwamnati ba akwai bukatar mu tashi tsaye wajen sanya ido ga yaran mu masu tasowa, domin gurbacewar rayuwar su babbar illace gare mu, hakan zai sa munanan abubuwa su yi ta faruwa.


Advertisement
Click to comment

labarai