Connect with us

LABARAI

Mun Kashe Dala Biliyan 9 Wajen Gine-gine –Gwamnatin Nijeriya

Published

on


Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce, ya zuwa yanzu ta kashe Dala Biliyan 9 wajen manyan aiyuka a kasar nan tun data dare karagar mulki a shekarar 2015.

Gwamnatin ta ce, wadannan gine-gine zasu tabbatar da bunkasar ci gaba da harkar yawon shakatawa.

Ministan watsa labarai da al’adu Mista Lai Mohammed ne ya bayyana haka a taron manema labarai domin kaddamar da fara taro na 61 hukunar “United Nations World Tourism Organisation Commission for Africa (UNWTO-CAF)” ranar Lahadi a Abuja babban birnin tarayya Nijeriya.

Taron da za a fara ranar 4 ga watan Yuni ana sa ran kammalawa ranar 6 ga watan Yuni, taken taron dai shi ne,”Tourism Statistics: A Catalyst for Debelopment.”

Ministan ya ce, ba za a taba samun cikakken amfanin yawon shakatawa ba ba tare da gine gine ba a kasa.

Minista Lai Mohammed ya ce,, “Harkar yawon shakatawa ba zai taba mutuwa a Nijeriya ba saboda banbance banbancen da ake dashi na kabilu da al’adu, haka kuma harkar yawon shakatawa na gaggawan samar wa da jama’a aikin yi”.

“Muna da mutane fiye da Miliyan 180 tare da kabilu daban daban har 250, kowanne da tarihinsa daban dana dayar, saboda haka harkar yawon shakatawa zai ci gaba da bukasa matukar a kwai gine gine masu ban sha’awa” inji Ministan.

Ministan ya kara da cewa, Nijeriya zata yi amfani da wannan taron waje tallatawa duniya cewa, lallai kasar nan nada cikkaken aminci ga ‘yan kasar da masu yawaon shakatawa da kuma masu zuba jari.

“Ya zuwa yanzu, mun samu tabbacin malartar taron daga kasashen waje 166 da ministoci 26 da kuma masu halartar daga cikin gida 332,” inji shi.

Daga nan ya kuma ce, dukkan abubuwan da ake bukata na bunkasa harkar yawon shakatawa muna da shi a Nijeriya, yana mai cewa, take taron ya yi dai dai da hankoron Nijeriya na bunkasa harkar yawon shakatawa a kasar nan.

Ministan ya kuma kara da cewa, Nijeriya ita ce, ta 24 a duniya wajen sakaka hanyoyin gudanar da harkar kasuwanci a duniya, hakan kuma ta matukar taimakawa a wajen jawo masu zuba jari cikin kasar nan.

Haka kuma, Sakataren kungiyar majalisar dinkin duniya ta “World Tourism Organisation (UNWTO),” Zurab Pololikashbili, ta ce, makasudin kafa majalisar dinkin  duniya shi ne kawar da talauci a fadin tarayya kasashen Afrika.

Ya kuma ce, hanya mafi sauki nay aka talauci shi ne kirkiro sabbin aiyukanyi kuma a bayyana lamarin yake cewa, ba za a aiya samar da aiyukan ba ba tare da an samar da ilimi ga dimbin jama’armu ba.

Mista Pololikashbili ya ce, majalisar dinkin duniya na kokarin tallata Nijeriya da sauran kasashen Afrika domin jawo masu zuba jari ta yadda za a samu ci gaba mai dorewa a nahiyar gaba daya.

Ya ce, a shekaru masu zuwa Afrika zata dogara ne a kan harkar yawon shakatawa gaba daya, hakan kuma zai samar da dimbin aikin yi ga daukacin nahiyar gaba daya.


Advertisement
Click to comment

labarai