Connect with us

LABARAI

Manu Soro Ya Sadaukar Da Albashin Sa Ga Al’ummar Da Gobara Ta Abka Musu

Published

on


Mai tallafawa Gwamnan Jihar Bauchi kan ayyukan kungiyoyin da bana Gwamnati ba Alh Mansur Manu Soro ya kai tallafin jin kai ga al’umar garin Marbini dake karamar Hukumar Ganjuwa wadanda iftila’in gobara ta abka musu har gidaje kimanin talatin da dukiya ta dubban naira suka kone kurmus inda ya sadaukar da albashinsa na watanni biyu domin tallafa musu.

Alhaji Mansur Manu Soro ya dauki  zuwa garin domin ganewa idonsa barnar da gobarar tayi da kuma jajantawa inda ya nuna alhini da jimami ga wannan jarrabawa da ta samu al’umar Marbini da sauran wurare da ke yankin.

Bayan ya zaga dukkan gidajen da gobarar ta kona ya miaa musu gudunmawar tabarmai da kudi a kowanne gida inda ya bayyana cewa ya sadaukar musu da albashin sa na watanni biyu don a kara samun kudin sayen kayan da za a tallafa musu. Ya kara da cewa ya kadu sosai a lokacin da ya ji labarin aukuwar gobara a garin don

haka ne yaga ya zama wajibi yazo da kansa ba aike ba don jajanta musu da ba su tallafin.

Da yake jawabi, Sarkin Marbini Alhaji Ya’u Ibrahim ya nuna matukar godiyarsa da jin dadi game da  wannan ziyara da taimakon jin kai da Alhaji Mansur Manu Soro ya kawo musu. Inda ya ce abin a yaba ne  wannan sadaukarwa ga al’uma na bayar da tallafi da ya yi saboda sun jima suna jin labarin taimako da tausayawa da yake yiwa talakawa sai gashi yau sun gani da idonsu don haka ya yaba kuma ya bukaci mutane su rika tausayin na kasa da su kuma ya kiraye shi da ya ci gaba da irin wannan hali mai kyau.

Shi ma da yake maida jawabi a madadin wadanda gobarar ta afkawa Mallam Sa’idu Ya’u Marbini yace basu da kalmar daza ta wadatar wajen nuna godiyarsu ga Alhaji Mansur Manu Soro sai dai su ci gaba da yi masa adduar Allah ya saka masa da mafificin alkhairi.

Sai dai akan hanyarsa ta dawowa Bauchi daga garin na Marbini, daruruwan mata da matasa sun yi dandazo a a garuruwan Ganjuwa,Gandu, Kafi-radi inda suka yi ta wakokin  jinjina ga Mansur Manu Soro da Gwamna  Abubakar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da daga hotunansu. A dukkan garuruwan, mai tallafawa gwamnan ya fito inda ya gana da al’uma ya kuma tabbatar musu da kudirin Gwamna  Abubakar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da kawo shirye-shirye domin tallafawa mata da matasa.

Al’umomin wadannan garuruwan sun kara jaddada bukatar su na ganin Mansur Manu Soro ya fito takara don wakiltarsu a majalisar tarayya saboda ganin irin taimakon da ya ke musu, inda shi ma ya amsa musu da cewa zai yi nazari kan batun.

 


Advertisement
Click to comment

labarai