Connect with us

LABARAI

Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Rage Kudin Kujerar Hajji Na Bana

Published

on


Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi ta sanar da rage yawan kudin kujerar tafiya Ibadar hajji na wannan shekarar, hukumar ta ce a bana 2018 kowani mahajjacin da zai tafi a karkashin hukumar a jihar Bauchi zai biya kudin tafiya naira miliyan daya da dubu dari hudu da saba’in da shida da naira dari uku da ashirin da takwas da kwabo casa’in da daya 1,476,328,91 a matsayin kudin kujerar aikin hajjin bana.

Babban sakataren hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi Abdullahi Magaji Hardawa shi ne ya sanar da rage farashin a wani taron manema labaru da suka kira a jiya, inda ya bayyana cewar ragin na zuwa ne a sakamakon kokarin da hukumarsu da hadin guiwar gwamnonin jahohi suka yi don ganin an sauwake wa masu tafiya aikin hajji a kowani lokaci.

Ya ce; “Idan kun tuna a shekarar bara Alhazai sun biya kudin kujera har naira miliyan daya da dubu dari biyar ashirin da shida a matsayin kudin kujera na aikin hajji 2017. Wannan kudin jama’a da dama sun yi ta korafin ya yi yawa, a bisa haka ne hukumar Alhazai ta kasa da hadin guiwar gwamnoni suka tashi tsaye wajen ganin an samu ragi kan yawan kudin kujera. A jihar Bauchi an rage daga 1.5 da dauri, yanzu a bana miliyan daya da dubu dari hudu da saba’in da shida da naira dari uku da ashirin da takwas da kwabo casa’in da daya 1,476,328,91 ne kowani mai niyya zai biya a matsayin kudin kujerar aikin hajjin bana,” A cewar shi.

Magaji Hardawa ya shaida cewar farashin da aka biya a wancan shekarar da kuma irin kokarin da aka yi abun a jinjina wa gwamnan jihar Bauchi ne, domin shi kadai ne ya zage ya biya kudin masaukin mahajjata kusa da wajajen gudanar da ibada wanda hakan ya sauwake wa alhazan da suka tafi daga jihar, don haka ne ya shaida cewar a bana ma gwamnan ya yi wannan hubbasawar tasa, don haka ne ya bayyana cewar gwamnati ta yi kokari kan biyan kudin masaukin alhazai.

Da yake bayani kan wadanda suka rigaya suka biya kudin ajiya na miliyan daya da rabi ya shaida cewar kowani Alhajin da ya biya wannan ya zo ya amshi sauran kudinsa daga hukumar, “Kasantuwar kudin kujeran aikin hajji ya sauko a bana, duk wadanda suka biya kudin ajiya suna da rarar kudi da za mu dawo musu da kayansu da ya kai dubu 23,671,” In ji Magaji.

Don haka ne ya shawarci dukkanin wadanda suka biya kudin su je cibiyoyin da suka biya domin amsar kudinsu da ya rage.

Har-ila-yau, Sakataren hukumar Alhazai na jihar Bauchi ya bayyana cewar wa’adin rufe saida fom da amsar kudin kujerar hajjin bana zai kasance daga ranar 21 ga watan nan da muke ciki, don haka ne ya bayyana cewar dukkanin mai niyya ya hanzarta zuwa domin biyan cakken kudi domin samun kujerar tafiya hajji a wannan shekarar.

Haka zalika hukumar ta yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga dukkanin wadanda suka samu sauke farali a shekara ta 2016 da 2017 da cewar akwai kudadensu da aka dawo musu da su daga kasar Saudiyya don haka kowani Alhaji ya hanzarta zuwa domin amsar hakkinsa “Kudaden da aka amsa domin a yi wa Alhazai hidimomi da ba a samu yi musu ba; an dawo da kudaden tuni kuma muka fara maida wa jama’a. amma har yanzu muna da sauran mutanen da basu zo sun amshi kudadensu ba. a shekara ta 2016 muna da kudaden mutane su 443 da basu zo sun amshi kudadensu ba. haka a shekara ta 2017 muna da Alhazai 57 da basu zo suka amshi kudadensu ba don haka muke sanar da su so zo su hanzarta amsa,” In ji Alhaji Hardawa.

Ya ce, dukkanin wani Alhajin da bai zo ya amshi kudinsa ba zuwa karshen watan shida (watan da muke ciki) za su kwashi sauran kudaden gami da maidawa ofishinsu na kasa wanda ko kowani sai dai ya je can ya amsa.

Hardawa ya kuma gargadi dukkanin wadanda aka basu fom amma basu kai ga dawo da fom din ba, ya shaida cewar su hanzarta dawo da fom din tun kafin a rufe amsa, ya shaida cewar idan aka rufe amsa ba za su samu tafiya ba kuma kudin da suka biya sai bayan an dawo gabanin a dawo musu da shi, don haka ne ya ce su yi amfani da damar da suka samu domin cike dukkanin sharudan da ake bukata daga garesu.

Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa ya shaida cewar biyan da kuma cike kowani sharadi a kan lokaci shine kawai zai baiwa hukumarsu damar cike kowani sharadi da aka gindaya musu daga hukumarsu ta kasa da kuma sharudan kasar Saudiyya, don haka ne ya nemi hadin kai daga masu niyya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai