Connect with us

LABARAI

Harin Offa: Babu Yadda Za A Yi Na Kulla Wa Jama’a Ta Irin Wannan Abu –Saraki

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya karyata zargin da ‘yan sanda ke yi masa na cewa, wasu daga cikin ‘yan fashin da ta kama wadanda kuma take zargi da aiwatar da mummunan fashin bankunan nan da a aka yi a watan Afrilu 2018 a garin Offa, inda aka kashe mutane 30, sun tsomo sunansa a cikin maganan.

Cikin wata sanarwar mannema labarai da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Yusuph Olaniyonu, ya sanya wa hannu, Shugaban Majalisar ta Dattawa, ya dage a kan cewa, ba ta yadda za a yi ya kasance cikin aikata fashi da makami sannan kuma ma akan mutanansa.

“Hankalin Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya kai ga wani labari da ke yawo a kafafen yada labarai na yanar gizo, wanda ya samo asali daga wani taron manema labarai da Kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa, Moshood Jimoh, ya yi inda yake alakanta shi da fashin da aka yi a garin Offa.

“Dakta Saraki yana bukatar daukacin al’umma da su yi watsi da wannan zargin maras tushe wanda wata sabuwar makarkashiyar ce da ‘yan sanda ke yi na bata masa suna ta kowace hanya.

“Ya kamata kowa ya sani, babu dalilin da zai kai ni yin fashi da makami sannan kuma ma wai a kan al’ummata.

“Lokacin da aka yi fashin na garin Offa, ni ne jami’in gwamnati na farko da ya ziyarci garin, kuma ma nan take a fadar Sarkin garin na daga waya na kirayi shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, inda na bukace shi da ya yi wani shirin samar da tsaro na musamman kamar yanda mutanan garin suka nema.

“Ya kamata mutane su tuna cewa a ranar 16 ga watan Mayu 2018, na ankarar da Majalisar Dattawa kan wani labari da na samu daga gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abdulfatai Ahmed, kan wani kulli da shugaban ‘yan sandan na kasa, Mista Ibrahim Idris, ke yi na shirya mani wani tuggu, ta hanyar wasu da suka kama suke zargin su da ayyukan kungiyar asiri a Ilorin, na kokarin sanya sunana a cikinsu. Wanda mun tabbata fallasan makircin kan lokaci ne ya bata wannan tuggun, yanzun kuma sun sake bullowa ta hanyar fashin garin Offa, suna son yin amfani da shi a kaina.

“An shirya wannan tuggun ne domin a kunyatar da ni, wannan kuma shi ne hucewan fushin Shugaban ‘yan sandan na kasa a kaina, kan kin amsa gayyatar da muka yi masa a Majalisa, inda muka neme shi da ya zo ya yi mana bayanin yawaitan kashe-kashe da rigingimun da ke aukuwa a ko’ina cikin kasarnan.

“Kamar dai yadda suka shirya na farkon a kaina ya watse ba tare da cinma burinsu ba, wannan ma watsewa zai yi, domin ina da tabbacin ba ni da kowace irin alaka da wasu gungun batagari.

“A matsayina na mutumin da yake matukar girmama dokokin kasa da dukkanin hukumce-hukumcen tsarin mulki, a duk lokacin da ‘yan sanda suka kawo mani goron gayyata a shiye nake da na karba kiran nasu ba tare da bata lokaci ba.

“Sai dai babban abin bakin ciki ne, a yi amfani da binciken masu laifi da nufin dagula aikin Majalisa don hana ta gudanar da aikin da ya hau kanta, wannan babban barazana ne ga tsarin dimokuradiyyanmu,” in ji sanarwar shugaban Majalisar ta Dattawa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai