Connect with us

LABARAI

Dalilanmu Na Zaftare Alawus Din Wasu Ma’aikata -Gwamnatin Bauchi

Published

on


A Jiya ne gwamnatin jihar Bauchi ta hanun ofishin shugaban ma’aikata na jihar Bauchi suka yi wa manema labaru bayani dalla-dallah kan makasudinsu na zaftare wasu kaso na Alawus din ma’aikatan jihar na watan Mayu.

Gwamnatin ta bayyana cewar matsalolin sun fara taso ne a sakamakon fara amfani da wani sabon tsarin da zai tsaftace hidimar albashi da kuma sahihan ma’aikatan jihar wato ‘Human Resources Management Information System’, wanda suka yi imanin hakan zai kawo karshen ma’aikatan ‘yan bunburutu a jihar.

Da yake zayyana bayanin wa ‘yan jarida a sakatariyarsu jiya, shugaban ma’aikatan Bauchi wanda Daraktan tsare-tsaren aiki na ofishin shugaban ma’aikatan jihar, Isyaka Tijjani wanda kuma shine ke kula da sabon tsarin fasahar biyan albashi da suka bullo da shi a jihar, ya bayyana cewa dukkanin wani ma’aikacin da aka zaftare masa Alawus hakan ya biyo bayan rashin kai amsar adadin alawus da ya kai inda ke amsa ne.

Ya ce; “Wasu mun lura suna amsar Alawus din da a gaskiya ba sune ya kamata su amshi wannan adadi na alawus din ba. kuma wasu suna amsar alawus din fiye da yadda ya kamata a basu. Wasu kuma masu karban alawus din nan suna amsa ne amma babu takarda daga gwamnati da ta amince a amshi wannan alawus din. Wadannan ne aka ciccire,” In ji Daraktan.

Tun da fari ma, Darakta Isyaka Tijjani ya yi bayani cewar wasu ma’aikata da dama sun rasa albashinsu a sakamakon kuskuren fara aiki da sabon tsarin da aka samu, amma ya shaida cewar za su biya kowani ma’aikaci kudinsa, “Bayan biyan albashin watan Mayu, an samu korafe-korafe masu yawa, wasu ba su samu albashinsu ba gaba daya, wasu kuma an yanke musu wani kaso na kudin da suke amsa.

“Abun da ke faruwa, gwamnatin jihar ta shiga wani sabon tsari na yadda za a tafi daidai da tsarin duniya wajen tafiyar da ma’aikata. a da sai ka samu ma’aikaci na amsar albashi amma idan ka je ka tambayi a wace ma’aikata ke aiki ba za ka samu ma’aikatar da ya fito ba.

Don haka ne sai gwamnati ta yanke shawarar maida hidimar biyan albashi ta hanyar amfani da takadar bayanai na ma’aikata daga kowace ma’aikata, da wannan takardar kowace ma’aikata yanzu za a ke amfani wajen biyan albashin ma’aikatan jihar domin dakile masu amsar albashi alhali ba ma’aikata ba ne, ko kuma wasu sun yi ritaya amma ba a dakatar da albashinsu ba,” A cewar Tijjani.

Shugaban ya bayyana cewar a wannan gabar ne kuma aka samu matsala a wajen fara amfani da wannan sabon tsarin, yake mai cewa “Matsalolin da aka samu sune, ka san wasu ma’aikatu suna da girma, suka fitar da sunayen ma’aikata amma basu iya sun sanya sunan ma’aikatansu dukka a cikin jadawalin da suka bamu ba, wasu kuma sun samu matsala ne da bankinsu,” in ji shugaban ma’aikata ta bakin Darakta a ofishin.

Daga bisani shugaban ma’aikatan ya shaida cewar dukkanin wani ma’aikacin da  matsalar rashin samun albashinsa ko kuma wadanda aka zaftare musu albashinsu da su yi hanzarin sanar da gwamanti ta hanyar da ta dace domin binciko inda matsalar take domin magancewa, yana mai shaida cewar dukkanin ma’aikacin da bai samu albashinsa da zarar ya gabatar zai samu albashinsa daga nan zuwa karshen watan da muke ciki.

Ya ce, “Yanzu haka ma’aikatan ofishina suna nan suna ci gaba da aiki a kan wannan lamarin, dukkanin wani ma’aikacin da ya gabatar da sunansa za a bincika a gano inda matsalar take, daga nan zuwa karshen watan June kowani ma’aikaci zai ga albashinsa,” In ji sa.

Sai dai kuma gwamnatin jihar ba ta yi bayyana adadin ma’aikatan da wannan matsalar ta shafa ba, domin kuwa shugaban ma’aikatan ya bayyana cewar har zuwa yanzu suna ci gaba da samun korafe-korafe don haka basu kai ga kammala tantance adadin ma’aikatan da basu samu albashinsu ba da kuma wadanda aka cire musu wani kaso daga Alawus dinsu.

Haka shi ma, shugaban hadakar kungiyoyin kwadago ta jihar Bauchi (NLC) Hashimu Muhammad Gital cewa yake yi a kungiyance sun tashi tsaye tun bayan faruwar lamarin wajen ganin kowani ma’aikacin da matsalar ta shafa ya samu hakkinsa kamar yadda ya dace.

“Mun cimma matsaya bayan da muka yi zama da dukkanin wadanda lamarin ta shafa. Yanzu haka an cimma matsayar cewar za mu ci gaba da fadi tashin har sai kowani ma’aikaci ya samu hakkinsa, domin wasu an samu matsalar ne a sakamakon matsalar na’ura, wasu kuma matsalar da aka samu na shigar da sunansu. Don haka za mu bi komai domin a samu mafita,” In ji Gital.

Dangane da reshe-reshe da suka yi barazanar tafiya yajin aiki dangane da wannan matsalar kuwa, shugaban kwadago ya bayyana cewar an yi zama da dukkanin rassa domin ganin kowa an yi masa adalci “Su wadannan kungiyoyin da suka bayar da wa’adi na tafiya yajin aiki ai suma suna karkashin kungiyar kwadago, kuma tare da su aka yi zama da gwamnan jihar Bauchi kuma tuni aka fara shirye-shiryen gyara matsalolin, don haka za su jingine wa’adin da suka diba wa gwamnati har a samu kawo karshen matsalar,” In ji Gital.

Dangane da masu korafin kan cewar kungiyar kwadagon ma tana biye wa gwamnati ya shaida cewar suna nan kan bakarsu a kowani lokaci, “Ga mataki dai mun dauka, da ba mu daukan mataki da basu zo sun ce mu yi zaman da su ba. kuma dukkanin kungiyoyin nan da su aka yi zama, matsayar da aka cimma tare da su aka cimma to wani rashi kuma ake magana a kai?,” A cewar shugaban NLC na Bauchi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai