Connect with us

LABARAI

Aikin Hajji: An Tsawaita Lokacin Kulle Karban Kudi Daga Masu Aniyar Sauke Farali

Published

on


Hukumar kula da aikin hajji ta kasa, (NAHCON), ta tsawaita lokacin da ta ajiye na yin rajista da kuma karban kudin kujera daga masu niyyan sauke faralin na wannan shekara ta 2018.

Daraktan tsare-tsare da bincike na hukumar, Sulaiman Usman, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa dukkanin shugabannin hukumar da Sakatarorinta a Jihohi a ranar 24 ga watan Mayu.

Usman ya ce, an umurci dukkanin hukumomin alhazan na Jihohi da su tabbatar da sun mika sunayen alhazan nasu na wannan shekarar zuwa ga shalkwatar hukumar kafin ko nan da ranar 30 ga watan Yuni.

“An umurce ni da in sanar da ku cewa an tsawaita lokacin rufe karban kudaden sauke farali na wannan shekarar zuwa 30 ga watan Yuni,” in ji Usman.

Ya kuma godewa dukkanin hukumomin alhazan na Jihohi da sauran kungiyoyi kan hadin kan da suke baiwa hukumar wajen dawainiyar ta na kai bakin na Allah zuwa dakin Allah.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, (NAN) ya kawo rahoton da ke cewa kimanin masu aniya 95,000 ne daga Nijeriya za su sadu da ‘yan’uwansu Musulmi na sauran kasashen duniya milyan biyu domin sauke faralin na wannan shekarar ta 2018 a kasar Saudiyya.

Ya kuma roki al’umman yankin da su kwantar da hankulansu duk da tsokanan da ake yi masu, ya kuma gargade su da su guji duk wani shirin mayar da martani, inda ya ce, tuni sun sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki.

 


Advertisement
Click to comment

labarai