Connect with us

LABARAI

Yadda Mu Ka Tsara Ciyar Da Abincin Buda-Baki A Yobe –Kwamishina

Published

on


Kwamishinan lamurran addini a jihar Yobe, Muhammed Muhammed Barah, ya bayyana cewa ma’aikatar sa tayi kyakkyawan tsarin yadda aikin ciyar da abincin buda-baki zai gudana cikin nasara. Ya ce, akwai karkkarfar kwamitin da yake shugaban ta, manyan kwamitoci daga shiyoyi guda uku dake jihar, kana kuma da a kowacce karamar hukuma, domin samun nasarar aikin.

“Kuma domin samar da daidaito da rage kalubale, shi ne muka rubuta wasiku zuwa ga kwamishinoni da yan majalisar dokoki, da muke dasu a nan jihar Yobe, kan su bamu sunayen yan kwamitin da zamu yi aiki dasu a matakin kananan hukumomi- wanda kuma sune muka damka raba kayan abincin a hannun su”.

Kwamishinan ya bayyana hakan a cikin tattaunawar sa da wakilin mu a jihar yayi dashi a ofishin sa, dake Damaturu, inda ya ce, a shekarar da ta gabata, domin su kawar da shakku a zukatan yan Nijeriya cewa zaman lafiya ya samu a jihar Yobe; ma’aikatar ta nemi amincewar gwamnatin jihar wajen tsara rabawa jama’a abincin buda-baki, wanda aka basu shinkafa buhu 1200 tare da naira miliyan 45.

Hon Muhammad Barah, ya bayyana cewa a wannan shekarar sun sake tura wa Gwamnan jihar bukatar ci gaba da aikin, wanda aka ware musu shinkafa buhu 1260 hadi da naira miliyan 65.5, da za a rinka raba abincin buda-baki a cibiyoyi 42; wanda ya ce idan an adadin shinkafar zuwa adadin cibiyoyin zai bayar da buhu 30 a kowacce cibiya.

“Bisa ga hakan muka kira su tare da basu buhun shinkafa 15 da jarkar man girki bakwai tare da kudi naira 424,000 a matsayin abin ciyarwar na kwanaki 15 a kowacce cibiya dake fadin wannan jiha ta Yobe. Yayin da a sauran kwanaki 15 na karshe ma haka abin ya gudana. Kuma kowacce cibiyar mun dauki mata uku da zasu dafa abincin”.

Kwamishinan ya kara da cewa, kimanin mutum 53 daga cikin ma’aikatan wannan ma’aikata ne zasu sanya ido a gudanar wannan aikin ciyarwa, tare kuma da basu kudin alawus-alawus na kwanaki 21 na aikin; idan ka cire kwanakin hutu biyu-biyu a kowanne mako.

Ya ce a bara suna da cibiyoyi 32 ne, amma bayan korafe-korafen da suka biyo baya ne shi ne suka kara 10 a kai. Sannan ya ce”muna da babban kwamiti mai mutum 10- wanda nine shugaban sa sai sakataren din-din-din mamba, daraktan zakka a matsayin sakatare, shugaban kwamitin sha’anin addini a majalisar dokoki, da mai ba gwamna shawara a lamurran addini, duk mambobi ne na wannan kwamitin”.

“Sannan a cikin kowacce shiyoyin uku da muke dasu a Yobe muna da kwamiti mai mutane tara(9), a karkashin daraktocin mu, wadanda zasu rinka bamu rahotanin abubuwan da ke wakana dangane da wannan aikin, tare da daukar matakin gaggawa bisa kan kowacce matsala.” Inji shi.

“Sannan kuma muna kira gare ku a matsayin ku na yan jaridu kan cewa ku kula da masu kokarin shigar da siyasa a cikin wannan lamarin ciyarwar, sam ba daidai bane”.

Haka zalika kuma, sun fito da sabon tsari sabanin yadda yake a baya- wanda a baya hatta dabbobin yanka da sauran wasu kayan masarufi, sai ka zo nan zaka karba, amma a wannan karon muka ce su je yankunan su su saya, saboda haka sai muka ba su kudin dabbobi da kayan masarufin, kuma wannan zai taimaka wa yan kasuwar yankunan su.

Ya ce ba su da hannu wajen nada wadannan kwamitoci a kananan hukumomi- aiki ne na kwamishinoni da yan majalisar dokoki na wannan jiha.

Ya kada baki tare da cewa, nan Damaturu akwai cibiyoyi hudu- kofar Fada, Islamic centre, school of nursing, Bra-bra kuarter, inda suma miskinai (guragu, makafi…) suka koka kan cewa an maishe su saniyar ware, inda a bana suma an ware musu tasu cibiya a ma’aitakar sannan a kai musu, abinda ya dan rage kuma sai a raba wa almajirai.

Ya ce an kikiro da wannan tsari na ciyarwa ne ga masu karamin karfi a cikin al’umma, saboda haka ko ka mallaki miliyan 100, matukar aka gan ka a layin karbar abincin, to ka nuna wa duniya kai maras karfi ne. Ya ce “Duk da ko nima da wannan abincin nake buda-baki, amma nayi haka ne domin in nuna wa duniya cewa ba abin kashi bane”.

“Ka ga kenan kowacce rana ana dafa buhun shinkafa 42, kuma mun bayar da kudin da za a sayi rago ko tinkiya ko taure babba, a yanka a kowacce cibiya- wanda a kalla kowanne mutum daya zai samu yanka biyu ko uku na nama. Kuma idan ka dafa kowanne buhun shinkafa daya zaka daro (tiren abinci) takwas, kowanne tiren abinci daya zai kwassar da kato biyar. To ka ribanya wannan adadin sau 42 ka ga mutum nawa ake baiwa abincin buda-baki, cikin kowacce rana?”

“Mu na kira ga masu hannu da shuni wajen taimakon maras karfi kamar irin wannan muhimmin aiki na ciyarwa da Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ya bamu umurnin yi a wannan jiha tamu ta Yobe.”

“Ma’aikatar kula da lamurran addini a jihar Yobe muna mika godiya ta musamman ga mai girma gwamna- Alhaji Ibrahim Gaidam, dangane da wannan babbar sadaukarwa wajen bayar da abincin buda-baki ga jama’ar Yobe. Sannan tare da tallafin kudin alawus-alawus ga malluman mu masu tafseer wadanda suka doshi 500.”

“Yayin da kuma, a shekarar 2017 gwamna ya amince wajen ware wa wannan ma’aikata sama da naira miliyan 163 domin gudanar da ayyukan ta, da suka hada da gina masallatai da gyara tare da makarantun islamiyoyi. Wanda a wannan shekara kuma, daga watan Junairu zuwa yau an ware muna sama da naira miliyan 99,” ya bayyana.

 


Advertisement
Click to comment

labarai