Takaddamar Salah: Ramos Ya Canja Layin Wayarsa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Takaddamar Salah: Ramos Ya Canja Layin Wayarsa

Published

on


Rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos ya canja layin wayarsa dana matarsa sakamakon sakonni dayake karba wadada ake masa barazanar cewa za’a kasheshi.

Ramos dai ya jiwa dan wasan Liberpool, Muhammad Salah ciwo a kafadarsa a wasan karshe na cin kofin zakarun turai wanda aka buga a satin daya gabata tsakanin kungiyar ta Liberpool da Real Madrid a kasar Ukarine.

Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan da matarsa suna karbar sakonni a wayoyinsu na cewa za’a kashe su saboda raunin da dan wasan yayiwa Salah wanda kuma ake tunanin dan wasan bazai buga wasan farko ba na gasar cin kofin duniya.

’Yan sandan kasar Sipaniya dai sun samu rahoto akan lamarin kuma tuni suka fara bincike akai inda suka bayyana cewa duk wanda aka kama da laifin tura wani sako na barazana ga rayuwar Ramos sai ya dandana kudarsa.

Wakilin dan wasa Ramos ya bayyana cewa dan wasan da iyalansa basa cikin kwanciyar hankali tun bayan da abin yafaru sakamakon sakonnin da suke shiga cikin wayoyinsu saboda haka suna bukatar hukumomin tsaro susaka ido akan dan wasan.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Masar dai ta bayyana cewa dan wasa Salah zai dawo kuma zai buga gasar cin kofin duniya sai dai abune mai wahala dan wasan yabuga wasan farko da kasar zata fafata da kasar Uruguay a wasan farko.

Advertisement
Click to comment

labarai