Connect with us

LABARAI

Kungiyar Action Aid Ta Yi Taro Kan Inganta Rayuwar Yara

Published

on


Ganin yadda ake fama da matsalar lalacewar tarbiyyar yara a wannan lokaci, kungiyoyi masu zaman kan su da hadin guiwar gwamnatoci sun himmatu wajen ganin sun ci gaba da gwagwarmaya kan matsalar inganta rayuwar yara marasa galihu da hana tauyewa ko cin zarafin kananan yara da ke aukuwa cikin al’umna, wanda ya shafi kowane sashe na Nijeriya akwai irin tasa matsalar. A saboda haka ne kungiyar Fahimta a Jihar Bauchi da hadin guiwar kungiyar Action Aid mai samun tallafin kasa da kasa sun gudanar da taro a otel din Zaranda da ke Bauchi, domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan gyaran tarbiyyar jamaa domin kawo karshen wannan matsala a Nijeriya.

Taron an gudanar da shi don tunawa da yaran da ake cin zarafin su, tare da taya yara bikin ranar yara Wanda ke gudana ranar kowace 27 ga Mayu na kowace shekara a duniya. A saboda haka kungiyar ta Fahimta da Action Aid suka gudanar da taro a ranar litinin don tattauna matsaloli da kananan yara ke fiskanta wadanda suka shafi cin zarafin su yaran da tura su almajiranci a wuraren da da basu sani ba al’marin da ke jawo salwantar kananan yara ko lalacewan tarbiyyar su.

Hajiya Maryam Garba ce shugabar kungiyar Fahimta a jihar Bauchi. Ta bayyana cewa makasudin taron shi ne a fiskanci kalubalen da ake fiskanta game da cin zarafin kananan yara na azabtarwa da salwantar musu da rayuwa a kowane sashe na kasar nan. Musamman ganin yadda wasu iyaye ke tura yara almajiranci a arewacin nijeriya a kudu kuma ake azabtar da kananan yara bisa zargin maita yadda a wasu lokuta har ake kashe su ko lalata musu rayuwa bisa zargi maras tushe na cewa yaran suna maita sun cinye wani.

Maryam Garba ta kara da cewa yin sakaci da rayuwar kananan yara shi ne kashin bayan lalacewan tarbiyyar yara Inda har girman su yawanci su ke tashi da miyagun dabiu sakamakon tsangwama ko azabtarwa da suke fiskanta.

Don haka ta ce suka gayyaci gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar na jihar Bauchi da uwargidansa a wajen wannan taro kuma duk sun yi alkawarin daukar wannan shiri zuwa yankunan karkara don dakile wannan matsala wacce yawanci ke tasowa akasari daga yankunan karkara nusamman game da tura yara almajiranci da nufin samun karatun addini amma hakan yakan yi wahala ga yaran sai ko su gamu da lalacewan tarbiyyya su dawo cikin jama’a su zamo barazana.

Daraktar gudanar da shirin daga kungiyar Action Aid a Abuja wadanda suka shirya taron Hajiya Suwaiba Yakubu Jibrin cikin jawabinta ga manema labarai ta bayyana cewa akwai matsaloli a Nijeriya game da cin zarafin kananan yara lamarin da ya kamata gwamnati da shugabanni al’umma da iyaye su sa ido kan tarbiyyar kananan yara don ganin sun kasance a makarantun zamani don neman ilmi da kuma tashi cikin tarbiyyar da mutane za su amfana ba tarbiyyar da yara za su samu don ciyar da kasa gaba idan sun kasance mutane na gari. Shi ne zai taimaka su daina zama barazana ga alumma ta hanyar shaye shaye da sace sace har su zama manyan masu aikata laifi.

Don haka Suwaiba Yakubu ta ja hankalin iyaye da su kasance masu lura da tarbiyyar yaran su ta hanyar sanya su a makaranta da basu tarbiyyar da ta dace don ba a san irin baiwar da Allah ya musu ba, ta yiwu sune shugabanni da za a yi alfahari da su wata rana, idan aka tarbiyyantar da su aka ba su ilmi wanda zai amfanar da su. Musamman ganin yadda a yau duniya ta kasance masu ilmi ke cin moriyar al’amurra ba jahilai ko masu kawo koma baya ga kasa ba.

Suwaiba Yakubu ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba kungiyar Action Aid da fahimta za su fara shiga kananan hukumomi goma na Jihar Bauchi don fara aikin wayar da kan mutane game da yadda za a dakile wannan al’ada ta tura yara almajiranci wanda ke jawo matsala ta cutar da kananan yara inda suke ci gaba da rayuwa maras tabbas da zama cikin yunwa da tsiraici musamman a wannan Lokaci da mutane ke fama da talauci yadda ba su ciyar da Kan su ba ballantana a kawo wasu yara da nufin su ne za su rika ciyar da su.

Don haka ake watsi da yaran suke shiga cikin mummunar rayuwa tarbiyyar su ke lalacewan da dukkan alumma ke shan wahala daga gare su. Don haka ta bayyana cewa sun kudiri aniyar shiga cikin wannan aiki don haka suke bukatar mutane su bayar da goyon bayan su. Musamman idan sun gama da kananan hukumomi 10 za su koma sauran goma ya kasance aikin ya tabbata a kowace karamar hukuma ta Jihar Bauchi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai