Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Borno Na Shirin Rusa Gidajen Masha’a 26 A Maiduguri

Published

on


Gwamnatin jihar Borno na shirin rusa gidajen da a ke zargi da aikata masha’a da badala akalla guda 26 a babban birnin jihar, wato Maiduguri, wadanda su ka hada da otel-otel da kuma gidajen saukar baki da ma dukkan gidajen da su ka zama matattarar shaye-shayen da ke haifar da raunin kwakwalwa.

Akalla mata masu zaman kansu (karuwai) 52, hadi da wasu karin mutane 10 wadanda a ke zargi da ta’amulli da miyagun kwayoyi ne a ka cafke a birnin Maiduguri a cikin wani samamen da rundunar hadin gwiwa da jami’an tsaro ta musamman wadda gwamnatin jihar Borno ta kafa a karkashin ma’aikatar shari’a.

A cikin shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar ta kaddamar da kwamiti a karkashin antoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan, domin ya jagoranci kwamitin wajen tsarkake babban birnin jihar, Maiduguri, daga ayyukan badala da karuwanci da ta’amulli da miyagun kwayoyi hadi da manyan laifuka da dangoginsu.

Bugu da kari kuma, an dora wa kwamitin alhakin garkame ilahirin tashoshin mota wadanda ke gudana ba bisa ka’ida ba zuwa wurare na musamman da gwamnati ta tanada a cikin birnin Maiduguri.

Dangane da wannan ne, kwamitin Barista Kaka Shehu tare da gamayyar jami’an tsaro su ka fita rangadin tafi-da-gidan ka su ka kai samame a hatsabibiyar gundumar Galadima; unguwar da ta shahara a sheke ayar masu zaman kansu da masu ta’amulli da kwayoyin saka maye, wanda gwamnatin jihar ta kuduri aniyar rusa wuraren badalar da ke wajen.

Tuni dai gwamnan jihar, Kashim Shettima, ya baiwa mazauna wannan unguwar wa’adin makonni biyu da su kwashe nasu-ya-nasu su bar wajen.

Kamar yadda ya bayyana, Shettima ya ce gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne bayan la’akari da ta yi da hatsarin da guraren su ke da shi, wanda dole a dauki matakin tsaftace birnin Maiduguri daga kyankyashe sabbin masu aikata miyagun laifuka.

A na sa ran wannan aiki na rusau ya shafi gidajen kwanan baki 26 da ke birnin na Maiduguri, kamar su New Trabel Hotel, Gongola Hotel, Paragon Hotel, Chinners Hotel, Pampas Hotel, Fabour Hotel, Blue Sport Hotel, Sea Neber Dry Hotel, Fall Biew Hotel, Okonna Hotel, East Guest Hotel da Peace Hotel.

Sauran sun hada da Chicago Hotel, Charbos Hotel, Benue Hotel, New Trabeller 2 Hotel, Moonlight Hotel, Chobados Hotel, Chinners 2 Hotel, Wazobia Hotel, Barka da Zuwa Hotel, Barka da Zuwa 2 Hotel, Loyal City Hotel, Make We Fled Hotel, Fabour Land Hotel da Maintenance Hotel.

 

 

 


Advertisement
Click to comment

labarai