Connect with us

LABARAI

An Sake Kashe Mutum 23 A Garin Zanuka Na Zamfara

Published

on


Da sanyin safiyar jiya ne mahara dauke da makamai su ka kai wa kauyen Zanuka da ke karamar hukumar Anka cikin jihar Zamfara hari, inda su ka dinga harbin kan-mai-uwa-da-wabi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23.

Maharan, dauke da muggan makamai, bayan kashe mutane da su ka yi, sun kuma fasa kauyen sannan kuma su ka banka ma sa wuta, wanda yayi sanadiyyar mata da yara fantsama cikin daji, wadanda har zuwa hada wannan rahotan wasu ba a san inda su ke ba.

Shugaban karamar hukumar Anka, Hon Mustafa Gado, ya tabbatar da faruwar wannan hari kuma ya yiwa manema labarai karin bayani.

“Mun samu tabbacin kashe mutane 23 daga kauyen Zanuka da ke cikin Karamar hukumata sakamakon mahara da su ka dirar ma garin da misalin 7:00  na safe. A cikin mutane 23 da su ka kashe, mutum biyu ‘yan kauyan Danmagaji ne da ke cikin karamar hukumar Maru, wadanda su ka kawo dauki, don su na makwabtaka,” in ji shi.

Sai dai ya kuma bayyana cewa, su ba su san matakin da jami’an tsaro su ke dauka ba.

Wadannan hare-haren dai a karamar hukumar sun zama ruwan dare, don babu wani mako ko sati da ba za a kashe mutane ko garkuwa da su ba a nan kusa.

Don jin ta bakin rundunar ’yan sanda jihar Zamfara ta bakin kakakinta, wakilinmu ya kira wayarsa ba a dauka ba kuma ya tura ma sa sakon kar-ta-kwana, amma babu wani amsa har zuwa lokacin kammala hada rahoton.

 


Advertisement
Click to comment

labarai