Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Majalisar Wakilai Ta Yi Fatali Da Zabe Da Na’urar Kwamfuta

Published

on


A ranar Alhamis, Majalisar Wakilai ta yi fatali da shawarar yin amfani da na’urar Kwamfuta a babban zaben 2019 da ke tafe.

Sun yi tir da hakan ne sakamakon dokar da aka gabatar mata wanda ke neman yin gyara a kan dokar ta zabe.

Amma wakilan Majalisar sun yi na’am da yin amfani da na’urar tantance katunan zabe domin tantance masu kada kuri’un kafin zaben, a kowace tashar zabe a duk fadin kasarnan.

‘Yan Majalisun, a lokacin tattaunawar na su kan dokar, sun cire wannan gyaran da aka yi kan dokar zaben wurin da aka nemi sanya yin amfani da na’urar Kwamfutan a cikin dokar zaben.

Sun yanke shawarar yin watsi da na’urar Kwamfutan, inda su ka amince da na’urar tantance katin zaben domin tantance masu kada kuri’un, inda suka ce batun jefa kuri’ar tilas ne a yi shi kamar yadda aka saba a baya.

A lokacin tattaunawar na su, Wakilin Majalisar Chinda Ogundu, ya nemi ya kara sanya wani gyaran cikin dokar zaben, inda ya nemi a kafa dokar duk tashar zaben da na’urar tantancewan ta kasa gudanar da aiki kamata ya yi a dakatar da zaben har sai an kawo wata da ke yin aikin.

Amma sai hakan ya janyo korafi daga wasu ‘yan Majalisun, wadanda ke cewa, hakan zai kara kawo bata lokaci ne kadai.

Wakilan kuma, sun ba da shawarar soke duk wani dan takara da ya bayar da shaidar iliminsa na karya wajen cike takardunsa, sannan kuma Jam’iyyarsa ta biya tarar Naira miliyan daya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai