Connect with us

LABARAI

Mutum Miliyan 17 Ne Suka Bar Afirka A Shekarar 2017 – MDD

Published

on


Akalla mutum miliyan 17 ne suka bar nahiyar Afirka zuwa wasu nahiyoyin duniya, domin neman abinci a shekarar 2017 kadai, kamar yadda sabon rahoton Majalisar dinkin Duniya ya bayyana.

Hakanan rahoton ya bayyana cewa, mutane milyan 5.5 ne suka kwararo nahiyar ta Afrika daga sauran nahiyoyin duniya, sannan kuma akwai ‘yan gudun hijira da suka yi ta daura a cikin nahiyar ta Afirka kimanin miliyan 19.

Rahoton ya ce, yawaitan mutanan da suka yi ta yin daura a cikin nahiyar ta Afrika ya kara habaka tattalin arzikin nahiyar, rahoton ya bukaci al’umman duniya da su daina baza jita-jitan abubuwa marasa kyau kan ‘yan gudun hijirar.

Babban sakataren kwamitin Majalisar na, UNCTAD, Mukhisa Kituyi, ne ya fadi hakan sa’ilin da yake kaddamar da rahoton mai taken, “Our analysis shows this to be true for millions of African migrants and their families.”

Kituyi, ya kara da cewa, “Yanda mutane ke daukan batun ‘yan gudun hijirar musamman wadanda suka fito daga nahiyar ta Afrika ya yi tsauri sosai, domin an cudanya karya da gaskiya, wanda hakan ke kara dagula lamarin sosai.” Rahoton ya ce, kudaden da ‘yan gudun hijirar da suke komawa gida daga ciki da wajen nahiyar, ya haura daga dala bilyan 38.4 a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007, ya zuwa dala bilyan 64.9 a cikin shekaru biyu har ya zuwa karshen shekarar 2016.

Hakanan, ‘yan gudun hijirar su ke samar da akalla kashi 20 na kudaden shigar kasar Koddebuwa, kamar yadda lissafin ya nu na daga shekarar 2008, su na kuma samar da kashi 13 na ku]a]en shigar           kasar Rwanda a lissafin shekarar 2012.

Junior Dabis, jagoran masu shirya rahoton ya ce, su na da shaidar kusanta ta kud-da-kud, a tsakanin ‘yan gudun hijirar da harkar kasuwanci, wanda su ke duk tamkar abu guda su ke.

“Afrika ta kai matuka wajen samun canje-canje,” ya yi nu ni da yarjejeniyar kasuwanci a tsakankanin kasashen na Afrika da kuma izinin yin zirga-zirga a tsakanin al’ummar ta Afrika.

“Da wannan, rahoton ya bayar da gudummawa wajen samar da kyakkyawan fahimta kan ha]arin da ke tattare da kai komon na ‘yan gudun hijirar na Afrika dangane da sake fasalin tattalin arzikin nahiyar,” in ji Dabis.

Sai dai kuma, tare da yawan ‘yan gudun hijirar da ke karakaina da kuma ayyuka a cikin nahiyar ta Afrika, nahiyar ta Afrika tana da mafi yawan mutanan da aka tilasta wa barin gidajen su a sakamakon rigingimu da kuma annoba kala daban-daban.

Baya ga asarar ribar ci gaban da ake fuskanta da barin ‘yan gudun hijirar daga nahiyar ta Afrika, akwai kuma nauyin da }asashen da suke kwarara suke fuskanta, wanda hakan ke sanya ‘yan gudun hijirar masu yawa dogaro da gudummawar agaji da suke samu daga wasu manyan kungiyoyin bayar da agaji na duniya kadai,” in ji rahoton.

 


Advertisement
Click to comment

labarai