Connect with us

LABARAI

Mutum Miliyan 17 Ne Suka Bar Afirka A Shankara 2017 – MXD

Published

on


Aqalla mutum miliyan 17 ne suka bar nahiyar Afirka zuwa wasu nahiyoyin duniya, domin neman abinci a shekarar 2017 kaxai, kamar yadda sabon rahoton Majalisar xinkin Duniya ya bayyana.

Hakanan rahoton ya bayyana cewa, mutane milyan 5.5 ne suka kwararo nahiyar ta Afrika daga sauran nahiyoyin duniya, sannan kuma akwai ‘yan gudun hijira da suka yi ta xaura a cikin nahiyar ta Afirka kimanin miliyan 19.

Rahoton ya ce, yawaitan mutanan da suka yi ta yin xaura a cikin nahiyar ta Afrika ya qara havaka tattalin arzikin nahiyar, rahoton ya bukaci al’umman duniya da su daina baza jita-jitan abubuwa marasa kyau kan ‘yan gudun hijirar.

Babban sakataren kwamitin Majalisar na, UNCTAD, Mukhisa Kituyi, ne ya faxi hakan sa’ilin da yake qaddamar da rahoton mai taken, “Our analysis shows this to be true for millions of African migrants and their families.”

Kituyi, ya qara da cewa, “Yanda mutane ke xaukan batun ‘yan gudun hijirar musamman waxanda suka fito daga nahiyar ta Afrika ya yi tsauri sosai, domin an cuxanya qarya da gaskiya, wanda hakan ke qara dagula lamarin sosai.” Rahoton ya ce, kuxaxen da ‘yan gudun hijirar da suke komawa gida daga ciki da wajen nahiyar, ya haura daga dala bilyan 38.4 a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007, ya zuwa dala bilyan 64.9 a cikin shekaru biyu har ya zuwa qarshen shekarar 2016.

Hakanan, ‘yan gudun hijirar su ke samar da aqalla kashi 20 na kuxaxen shigar qasar Koddebuwa, kamar yadda lissafin ya nu na daga shekarar 2008, su na kuma samar da kashi 13 na ku]a]en shigar           qasar Rwanda a lissafin shekarar 2012.

Junior Davis, jagoran masu shirya rahoton ya ce, su na da shaidar kusanta ta qud-da-qud, a tsakanin ‘yan gudun hijirar da harkar kasuwanci, wanda su ke duk tamkar abu guda su ke.

“Afrika ta kai matuqa wajen samun canje-canje,” ya yi nu ni da yarjejeniyar kasuwanci a tsakankanin qasashen na Afrika da kuma izinin yin zirga-zirga a tsakanin al’ummar ta Afrika.

“Da wannan, rahoton ya bayar da gudummawa wajen samar da kyakkyawan fahimta kan ha]arin da ke tattare da kai komon na ‘yan gudun hijirar na Afrika dangane da sake fasalin tattalin arzikin nahiyar,” in ji Davis.

Sai dai kuma, tare da yawan ‘yan gudun hijirar da ke karakaina da kuma ayyuka a cikin nahiyar ta Afrika, nahiyar ta Afrika tana da mafi yawan mutanan da aka tilasta wa barin gidajen su a sakamakon rigingimu da kuma annoba kala daban-daban.

Baya ga asarar ribar ci gaban da ake fuskanta da barin ‘yan gudun hijirar daga nahiyar ta Afrika, akwai kuma nauyin da }asashen da suke kwarara suke fuskanta, wanda hakan ke sanya ‘yan gudun hijirar masu yawa dogaro da gudummawar agaji da suke samu daga wasu manyan qungiyoyin bayar da agaji na duniya kaxai,” in ji rahoton.

 


Advertisement
Click to comment

labarai