Connect with us

LABARAI

Mace Ta Daba Wa Mijinta Wuka Ya Mutu

Published

on


‘Yan Sanda a Legas sun kama wata malamar makaranta mai suna, Abimbola Olamide, bisa zargin daba wa mijinta, Dare Akinbobola, wuka wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa a cikin gidansu da ke Ikorodu, a can Legas.

Kamar yadda kafar yada labarai ta, an ruwaito cewa, an sami sabani ne a tsakanin ma’auratan biyu, wanda har lamarin ya kai ga fada a tsakanin su.

A cikin fadan na su ne aka ce, Olamide, ta daba wa mijin nata mai shekaru 28 wuka, wanda nan take sai ya mutu.

 

A cikin wani faifan bidiyo inda cikin sa take bayar da shaidar amsa laifin nata, matar mai ‘ya’ya biyu cewa ta yi ta yi hakan ne a kokarin da take na kare kanta.

Da take magana da harshen yarbanci cewa ta yi, “Ba da gangan ne na kashe mijin nawa ba. Duka na ne yake yi, a sabili da dukan da yake yi mani ne har ya fasa farantan tangaran da yawa a kaina. A baya ma ya sha lakaka mani dukan tsiya, amma a baya duk lokacin da yake duka na, sai na gudu na bar masa gidan.

“Amma a wannan karon kulle gidan ya yi don ya hana ni gudu, ya kwantar da ni yana ta duka na. Ba yanda na iya.

Sai na dauki wuka a kasa, nufi na, na tsoratar da shi da wu}ar. Sai na rike wukar, amma duk da hakan bai kyale ni ba. bisa kuskure ne na daba ma shi wukar, sam ba da gangar ne na kashe mijin nawa ba.

“Da jimawa iyaye na sun fa]a mani na rabu da shi, amma sai na ki, saboda shi ne mijina, shi ne kuma uban ‘ya’yana guda biyu. Ya kasance yana duka na, ka tambayi kowa ka ji, kowa ma ya san hakan. Hakuri kadai nake yi.”

Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin tuntuban iyalai da makwabtan mamacin bai yi nasara ba.

Sai dai bayanin na ta ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma a ranar Alhamis.

Yayin da wasu ke cewa, ya zama tilas ta fuskanci shari’a kan laifin da ta aikata, wasu kuwa cewa suke yi, ta na da uzuri a shar’ance.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas, SP Chike Oti, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce, “Wata matsalar ce ta inda wata ta kashe mijinta, matar ta soke shi da wuka ne a wuya inda a nan take shi kuma mijin ya fadi ya mutu.

“An kai gawar ]akin binkice, ita kuma matar an kama ta, an kai ta sashen kula da masu kisan kai da ke Yaba, domin ci gaba da bincike.”


Advertisement
Click to comment

labarai