Connect with us

LABARAI

INEC Ta Fara Raba Katin Zabe Na Dindindin A Bauchi

Published

on


Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Bauchi wato (INEC) ta bayyana cewar kawo yanzu dukkanin wani ko wata da ya yi rijistan katin zabe na dindindin daga ranar 27 na watan Afrilun 2017 zuwa Junairu 2018 katinsa na zaben ya fito yana iya zuwa ya amsa a hanun hukumar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Bauchi wato INEC Alhaji Ibrahim Abdullahi shine ya shaida hakan a jiya sa’ilin da ke ganawa da manema labaru a ofishin hukumar zabe da ke Bauchi.

Ya ke cewa, za su ci gaba da yin rijista wa jama’a har zuwa daf da gudanar da zaben 2019, “Hukumar INEC ta fara gudanar da yin rijistan katin zabe mai zaman na dindindin tun a ranar Alhamis 27 ga Afrilun 2017 har kuma zuwa karshen watan Disamban 2018 kamar yadda dokar zabe ta 2010 sashi na 9 zuwa 24 wanda aka yi wa kwaskwari,”

Kwamishinan ya bayyana cewar; “dukkanin wadanda muka yi musu rijista daga 27 na watan Afrilun 2017 zuwa watan Junairu 2018 mutane dubu casa’in da uku da dari hudu da tamin da shida (98.486) a jihar Bauchi yanzu haka katin zabe na dindindin ya fito. Da wannan katin ne za su samu nasarar dangawala wa dukkanin wadanda suke so a zaben 2019 da ke tafe, kamar yadda kuka sani babu PBC ba za ka yi zabe ba,” In ji Ibrahim.

Kwamishinan ya bayyana cewar tun a ranar Litinin 21 ga watan Mayu, 2018 ne suka kaddamar da fara raba katin zaben ga jama’a a jihar Bauchi a dukkanin fadin kananan hukumomi a jihar da suke jirar Bauchi.

INEC ta bayyana cewar har zuwa yanzu a kowace ranar Allah daga karfe takwas na safiya zuwa uku na kowace yammaci baya ga ranar hutu na Asabar da Lahadi suna ci gaba da aikin yin rijista wa jama’an jihar Bauchi a dukkanin cibiyoyin yin rijista da suka fitar a fadin jihar, don haka ne ya nemi jama’an jihar wadanda suka kai shekaru 18 basu da katin zaben su hanzarta domin yin wannan rijistan domin samun zarafin mallakar katin da zai basu damar zaban wadanda suke so.

Daga nan kuma, Ibrahim Abdullahi ya bukaci ‘yan siyasa, matasa, kungiyoyin jama’an, kungiyoyin mata, da su nuna halayen kwarai gabanin, lokacin da kuma bayan zaben 2019 da ke harararmu, yana mai shaida cewar duk wanda ya kauce wa hanya zai fuskanci shari’a.

Da yake karin haske wa manema labaru kan yadda jama’a basu zuwa amsar katin zabensu da kuma yin wannan rijistan, Kwamishinan zabe a jihar Bauchi ya daura alhalin hakan ga jam’iyyun siyasa, yana mai shaida cewar sakacinsu ne ummulhaba’isin irin wannan matsalar “Ni ina mamakin yadda za ka ga jam’iyyun siyasa suna shiga lunguna da sakona suna neman jama’a su zabesu a lokacin kamfen, amma ba za su iya shiga lunguna su fadakar da jama’a kan su mallaki katin zabe ba. Ta yaya ne masoyinka zai yi zabenka ba tare da katin da zabe nan?

“Don haka ina kira ga dukkanin jam’iyyun siyasa, da su tashi tsaye su fadakar da jama’ansu kan su mallakin katin zabe. Duk wanda ya san ya yi rijista to ya je ya amshi katinsa na dindindin, idan kuma mutum bai yi ba ya zo ya yi, domin ta haka ne kawai za ka iya faranta wa wanda kake so. Don haka jam’iyyun siyasa su tashi tsaye wajen fadakar da magoya bayansu kan mallakar katin zabe,” In ji Kwamishinan INEC Ibrahim Abdullahi.

Taron manema labaru wanda kuma ta hada da jam’iyyun siyasa daban-daban, inda suka samu zarafin yin tsokaci da kuma yin tambaya kan ababen da suka shige musu duhu a lokacin da INEC din ke warware mus


Advertisement
Click to comment

labarai