Connect with us

LABARAI

Dangote Ya Bayar Da Gudummawar Mota 150 Ga ‘Yan Sanda

Published

on


Shahararren dan kasuwar nan na Afirka Alhaji aliko Dangote, ya ba rundunar ‘yan sandan Nijeriya gudummawar mota dari da hamsin don su samu nasarar aiwatar ayuukan tsaro a kasar nan.

Gidauniyar bayar da tallafi ta Dangote wato Dangote Foundation c eta mika gudummawar ga jami’an rundunar ‘yan sandan shekaran jiya a Abuja.

Da yake bayani wajen mika wannan gudummawar shugaban Gidauniyar, Aliko Dangote ya nuna ya bayar da gudummar ce ga bangaren tsaron saboda muhimmancin da tsaron ke da shi wajen wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sannan kuma ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da jami’an tsaron orin wannan gudummawa matukar sun alkinta wannan.

Ya ce, “Dalilin haduwarmu a nan shi ne mu mika gudummawar motoci kirar salun guda 150 ga rundunar ‘yan sanda don a taimake su yadda za su samu damar gudanar da harkokin tsaron dukiya da lafiyar al’ummar wannan kasa”.

Saboda ganin babban kalubalen da gwamnati ke fuskanta wajen muhimman abubuwan rayuwa irin su ilimi da lafiya  da kuma tsaro, ya zama wajibi ga masu-hannu-da-shuni da su taimka mata yadda za a samu nasarar aiwatar da su.

Attajirin ya ce, Gidauniyar na bayar da gudummawa a kan bunkasa ilim da lafiya da tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa da taimaka wa wadanda wani bala’i ya afkawa.

Shi ma a nasa jawabin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yaba wa gidauniyar bisa irin tallafin da take bayarwa, sannan kuma bayyana godiyar gwamnatin tarayya ga Dangoten bisa irin taimakon da yake yi mata.

Ya ce bayar gudummawar wadannan motoci zai taimaka wa rundunar ‘yan sanda wajen yin yaki da masu laifuka, wanda haka kuma na nuna cewa, za a rage yawan aika laifuka, domin ‘yansanda za su samu damar shiga lunga da sako don hana aikata laifuka.

Haka kuma Osinbajo ya kara da cewa, babu wani mutum daya a duk fadin kasar nan day a tada bayar da gudummar mota 150, saboda Dangote shi ne mutum na farko da ya fara wannan babban aikin aheri, don haka muna gode masa a kan wannan kyakkawan abu da ya yin a taimaka wa al’ummar kasa.

Shi ma da yake na sa jawabin shugaban rundunar ‘yan sandan na kasa Ibrahin Kpotun-Idris, ya gode wa Gidauniyar bisa wannan karamci da ta yi musu,sannan kuma ya dauki alkawarin kula da motocin da kuma tabbatar da cewa sun yi aikin day a kamata su yi.

Saboda haka sai ya bukaci al’umma da su kyautata dabi’un a dukkan ma’amalarsu, su kiyaye dokar kasa, domin yanzu sun kara samun karfin da za su yaki masu laifi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai