Connect with us

RA'AYINMU

Published

on


Watan Azumi wata ne mai alfarma sakamakon cewa a ciknsa ne aka saukar da Alku’ani maigirma ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Dan’abdullahi domin shiriya ga dukkan halitta.

Azumi na zama nau’in bauta wa Allah ne wanda ke zama  wajibi a kan dukkan Musulmin da ya balaga kuma mai hankali da lafiya, wanda ake kame baki daga barin ci da sha da kuma saduwa da mace tun daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, na tsawon kwana 29 ko 30.

Ana fara Azumin ne ta hanyar ganin sabon wata Ramadan, yana kuma daya daga cikin shika-shikan Musulinci guda biyar. Haka kuma lokacin gudanar da wannan Azumi ana so mutum ya kara kaimi wajen bautar Allah domin neman kusaci da Allah, ta hanyar kara yawan ibada da kyawawan dabi’u da taiamaka wa mabukata.

Babban dalilin wajabta Azumin watan Ramadan ga al’ummar Musulmi shi ne su koyi darasi na juriya  da kuma tuna halin da wasu al’umma ke ciki. Allah (SWT) ya bayyana a cikin Alkur’ani cewa, Azumi na taimaka wa al’umma zama tagari. “Ya ku wadanda kuka yi imani an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka gabace ku domin ku koyi takawa da tausayawa” (Alkur’ani 2:13).

Watan Azumin Ramadan shi ne wata na 9, a cikin jerin watannin Musulinci guda 12, wanda kuma ke da daukaka, domin a cikinsa  akwai wani dare da ake cewa, daren Lailatul Kadari- Daren da aka saukar da Alku’ani a cikinsa, wanda Allah Ta’ala ya ce, wannan dare na Lailatul Kadari ya fi wata dubu. Saboda falalar wannan daren ma mutane kan kara dagewa wajen bautar Allah domin yin muwafaka da shi, wanda duk abin da ka roka a wajen Allah a cikin daren Allah zai amsa maka.

Bayan kammala azumin ne na tsawon kwana 29 ko 30 za a yi Eid-ul-Fitr (karamar sallah), wanda a wannan rana ce aka bukaci mawadata, su wadata marasa shi, yadda su ma za su kasance cikin farin ciki bayan kammala  sallar ta su. Domin kuwa yana daga cikin hikimar wajabta fitar da zakkar kono ga duk wanda Allah ya hore wa, bayan kammala Azumin.

Domin kuwa a ranar sallah ne al’ummar Musulmi kan kasance cikin farin ciki da murnar kamamla azumin lafiya ta hanyar wadatuwa da abinci da dinka sababbain kaya da kai ziyara ga ‘yan’uwa da abokan arziki.

Akwai darusa masu yawa da ya kamata a koya daga yin Azumi, domin kuwa ana so tarbiyyar da mutum ya samu lokacin azumi ta  dore a duk tsawon rayuwarsa. Ya ci gaba da yin ibada da hakuri da tausayawa da taimakawa kamar yadda yake yi lokacin Azumi.

Saboda haka, lokaci azumin watan Ramadan babbar dama ce da ya kamata al’umma su yi amfani da ita wajen samun ci gaban rayuwa a kowane lokaci.

Muna kuma taya dukkan al’ummar Musulmi zagowar wannan wata mai alfarma, da fatan Allah ya karbi dukkan ibadun da aka yi a wannan wata.

 


Advertisement
Click to comment

labarai