Connect with us

LABARAI

Zaftare Albashi Ya Tada Kura A Bauchi

Published

on


Kungiyar malamai reshen kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin Jihar Bauchi (ATAP) ta baiwa gwamnatin Bauchi wa’adin mako guda tak da ta gaggauta daidaita wa ma’aikatansu albashinsu biyo bayan zaftare albashin ma’aikatan jihar ta Bauchi na watan Mayu da gwamnatin jihar ta yi.

Haka kuma, kungiyar ta bukaci gwamnan Jihar Bauchi ya gaggauta tsige shugaban ma’aikatan na Jihar Bauchi, Alhaji Liman Bello a bisa abun da suka kira da kokarinsa na dakushe ci gaban aikin gwamnati a jihar.

Gargadin yana kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da suka fitar dauke da sanya hanun shugaban kungiyar ta malamai na ATAP, Kwamared Bala Mohammed Yakubu inda ya raba wa ‘yan jarida a jiya.

Tun da fari, kungiyar malamai na kwalejin ta tunatar da jama’an kan yadda suka sadaukar a lokacin da jihar take tsaka da mashashsharan matsalar tattalin arziki “Idan za ku iya tunawa, kungiyarmu ta sadaukar sosai wa jiharmu da kasa baki daya a lokacin da ake fama da mashashsharan tattalin arziki, domin zage damtse wajen tabbatar da cewar sha’anin ilimi bai fadi kasa ba, duk da halin da aka kasance a wancan lokacin,”

“Muna son mu tunatar da shugaban ma’aikata na Jihar Bauchi da ya tuna kan cewar tsarin biyan albashin kwalejin kimiyya yana nan ne a tsare kamar yadda ake tafiyar da shi bai-daya a kasa baki daya a kowace jiha,” In ji Kwamared Bala Mohammed Yakubu.

Suka daura da cewa; “Haka kuma, muna sake tunatar da shugaban ma’aikatan Jihar Bauchi da ya gane cewar a kwalejin Tatari Ali Polytechnics babu wani harkar alawus ta barauniyar hanya. Kwalejin tana da tsari wanda ya sha banban da sauran sashi-sashi da kuma bangarorin ma’aikatu a jihar,”

Kungiyar ATAP ta shaida cewar tsarin biyan ma’aikatanta albashi na tafiya ne daidai da kwarewar ma’aikaci da kuma girman mukaminsa, don haka ne suka nuna kaduwarsu gaya a bisa yanke musu kaso daga cikin albashin ma’aikata ba tare da sanarwa ko sanin makasudin hakan ba, suna masu shaida cewar babu wata ankararwa da gwamnatin ta yi musu kan hakan illa dai sun wayi gari da ganin albashinsu a kwakushe wanda suka bayyana hakan da cewar ya saba wa dokar aikin gwamnati.

Daga wannan gabar ne kuma suka baiwa gwamnatin jihar wa’adi ko kuma su tsunduma yajin aikin sai Illa-Masha-Allah “Muna watsi da batun rage albashin ma’aikata, muka kuma kira cikin gaggauwa a hanzarta daidai mana hidimar kudinmu da ake zaftarewa daga nan zuwa kwana bakwai ko kuma tafi yajin aiki,”

Kan wannan matsalar ne kuma suka yi kira ga gwamnan Bauchi ya tsige shugaban ma’aikata na Jihar Bauchi a bisa neman dakushe ci gaban aikin gwamnati a jihar, “Kungiyarmu tana yaba wa kokarin gwamnan Jihar Bauchi M.A Abubakar sosai a bisa biyan albashi da yake yi a kan lokaci. Bayan haka, muna masu kiran gwamnan da ya gaggauta cire shugaban ma’aikata na Jihar Bauchi a bisa kokarin da yake yi na yi wa gwamnati zagon kasa a kokarinta na daukaka darajar aikin gwamnati a jihar,” Kamar yadda shugaban ASUP reshen ATAP ya shaida.

Kungiyar ta ASUP reshen kwalejin ATAP dai kawo yanzu ta nuna fushinta kan cire wa ma’aikatanta kasonsu na albashin watan Mayu, ta kuma nemi gwamnatin cikin kwanaki bakwai ta dawo wa ma’aikatanta hakkinsu da aka cire musu domin tabbatar da aiki mai nagarta.

Wakilinmu ya shaida mana cewar ba kawai wannan sashin ba ne matsalar ta rutsa da su, kusan kowace ma’aikata da kuma kusan kowani ma’aikaci ne suka samu wannan matsalar kamar yadda muka kawo muku cikakken labarin a bugunmu ta jiya.

 


Advertisement
Click to comment

labarai