Connect with us

LABARAI

Fadama III Ta Kaddamar Aikin Kwashe Bola A Gombe

Published

on


Shirin Fadama na III ta kaddamar da kwashe Bola na jihar Gombe a unguwar Dawaki Ajiya dake fadar jihar inda aka zabi Matasa goma dan yin wannan aikin na wannan unguwa ta Dawaki masu suna Fadama Banguard.

Da yake jawabi a wajen wannan taro jami’in shirin na kasa, Mista Tayo Adewumi wanda Misis Busayo Awotunde, ta wakilci shi cewa ya yi wannan aiki na kayi a biya ka aiki ne wanda shirin Fadama na III ta bullo da shi dan taimakawa matasa.

Mista Tayo Adewumi, yace a madadin Ministan aikin Gona na Najeriya Cif Audu Ogbeh, ya jinjinawa gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo, na yadda yake bada tallafi a duk wani shirin Fadama.

Yace lailai gwamnatin jihar Gombe ta mayar da hankali sosai wajen ganin ta rage zaman banza da samarwa da matasa hanyoyin dogara da kai, sannan yace yana kuma yin mai yiwu wa wajen ganin ya farfado da wadanda rikicin ta’addanci na Boko Haram ya shafa.

A cewar sa a karo na biyu na shirin Fadama da ake kira Additional Financing AF II shiri ne da yake taimakawa cikin gaggawa na ragewa iyalan da suka shiga garari a jihohi shida na yankin arewa maso gabas musamman magidanta da rikicin boko haram ya shafa.

Mista Tayo Adewumi, ya kara da cewa wannan shiri ya gano yankunan karkara guda 67 da suke taimakawa a wani shiri na daban na CAPs Community Action Plan, wanda a sakamakon hakan kimanin magidanta dubu biyu da dari shida da tamanin ne suka amfana da tallafain kayan abinci, wanda ya kai kimanin mutane sama da 21,440 ne suka amfana kai tsaye da kashi 21 cikin dari Mata ne da sune suke jagorantar gidaje.

Daga nan sai yace wannan aiki na kayi a biya ka Cash-for- work an tsara shi ne da nufin magidanta dubu goma sha biyu su amfana a duk fadin shiyar arewa maso gabas a jihar Gombe kuma yankunan karkara 90 ne da mata da matasa dubu daya da dari takwas za su amfana.

A nasa jawabi kwamishinan Ma’aikatar aikin Gona na jihar Gombe Alhaji Dahiru Buba Biri, wanda manajan shirye-shirye ma’aikatar Laban Maina, ya wakilta cewa ya yi yana cike da farin ciki na yadda shirin Fadama ta bullo da wannan shiri na Fadama Banguard dan taimakawa matasa.

Dahiru Buba Biri, ya ce abunda ya fahimta da wannan shiri shine zai taimakawa wajen tsabtace muhalli zai kuma taimaka wajen samawa matasa aikin yi.

Sannan yace gwamnatin jihar tana farin ciki da wannan aiki na Fadama III suma suna yin nasu a gwamnatance da taimakawa shirin.

Ita ma shugabar shirin Fadama ta Gombe Habiba Muhammad, ta bayyana cewa a sanin ta wannan shiri na Fadama ya samar da yatsun susa musamman a tsakanin yan gudun hijira da suke tsakanin al’umma a jihar.

Habiba Muhammad, tace duka yankunan karkara dake kananan hukumomi 11 na jihar za su amfana da wani aiki na shirin Fadama da ya kama daga rijiyar burtsate ko kwalbati ko hanya ko a tona musu dam na kasa ko kuma a samar musu da kasuwa da sauran su.

Tace wannan shiri ba karamin taimakawa zai yi ba wajen kare muhalli wanda hakan ma yakan haifar da wasu cututtuka, amma tsabtace muhallin zai kara taimakawa wajen kara samarwa da al’ummar karkara lafiya.

Shugabar ta kara da cewa shirin yana da fuska biyu ne na samarwa da matasa aikin yi sannan kuma zai kawo tsabtace muhalli.

Wasu matasa biyu da suka ci gajiyar shirin yan unguwar Dawaki Ajiya, sun bayyana cewa masu kallon kamar aikin karanta ne kwashe shara dan basu samu ba amma su kan suna maraba da wannan shiri kuma za su rike shi hannu bibiyu.

Kowanne matashi zai dinga aiki naira dubu daya da dari biyar ne kullum wanda zai basu dama na samun hanyar dogaro da kan su.


Advertisement
Click to comment

labarai