Connect with us

LABARAI

Zaman Lafiya: Gwamnati Ta Tallafawa Mata Da Matasa Su Fita Daga Fatara –Maryam Garba

Published

on


An shawarci gwamnatin tarayya da na Jihohi a Nijeriya su fito da sahihan hanyoyin gaskiya don tallafawa mata da matasa fitar da su daga cikin halin fatara da yunwa wanda ke barazana mai girma wajen lalata tarbiyyar su, saboda matsalolin rashi da aka shiga sun taimaka wajen

cusa mata da matasa cikin miyagun halaye da suke barazana ga zaman lafiyar kasar nan.

Hajiya Maryam Garba shugabar kungiyar FAHIMTA masu rajin tallafawa mata da matasa game da yadda za su inganta rayuwar, ita ce ta bayyana haka cikin hirar ta da wakilin mu a Bauchi, inda ta bayyana cewa matsalolin kuncin rayuwa da aka shiga sun cusa mata da dama cikin miyagun hanyoyin neman abin da za su ci ta kowane hali yayin da suma matasa damuwar rashin karatu da rashin aiki ya sa suka shiga aikata miyagun ayyuka da shaye shaye wanda ke ci gaba da yin barazana ga zaman lafiyar kasa da mutanen ta.

Hajiya Maryam Garba ta kara da cewa “gaskiya a ko ina akwai matsala ta fatara da yunwa da rashin walwala don haka suke rokon Allah ya kawo mana rangwame saboda muna ganin wahalar da ake ciki, kuma a nan Bauchi akwai matsalar kwararowan ‘yan gudun hijra kusan a kowane gida akwai mutane da suka zo ake tallafa musu. A wannan fanni muna kokari akwai kungiyoyi da dama da muke shiga kauyuka da su muke wayar da kan mata game da rayuwa”, In ji Maryam Garba.

Ta ce misali a kauye za ka ga gida akwai zogale amma mata sai su rasa jini a jikin su ko su zauna da yunwa alhali ga ganyaye a kewaye da su a cikin gida wani lokaci basu san yadda za su sarrafa su ta sabbin hanyoyi na zamani su amfanar da lafiyar su ba. Don haka suke shiga yankunan karkara don wayar da kan mata game da yadda za su hada waken soya ya ba su sinadari na madara da yadda za su hada ganyaye da wake su canji nama a wajen kara kuzari da ci gaban lafiya.

Don haka ta nuna damuwa game da mawuyacin halin da mata da yara suka shiga na matsaloli da  ake fiskanta musamman wanda suka shafi yunwa da talauci da sauran wahalhalun rayuwa, don haka ta shawarci iyaye a lokacin da za su aurar da yara a rika jan hankalin mazaje ana nuna musu hakkokin da ke kan su a kowane lokaci musamman ya kamata irin fadan da ake yi wa mata don su zauna lafiya a gidajen su suma maza a musu wannan fada don su rike hakkomin mata da ke kan su.

Bayan haka kuma ta ja hankalin gwamnati da ta rika ware abubuwa na musamman da za a rika tallafawa mata da kudi wanda za su rika lura da kan su da yaran su kamar yadda ke faruwa a kasashen duniya da dama.

Saboda mata sun shiga mawuyacin hali ganin yadda wahalhalu ke tunkarar mutane maza suna gudu suna barin matan su don haka ya kamata a tallafi irin wadannan mutane don a samar da hanyoyi da tallafin gwamnati zai rika zuwa ga mata kai tsaye don su ci moriyar duk wani shiri da aka fito da shi domin su, musamman ya kamata a rika bude musu ajiyar banki

ana tura musu kudi kai tsaye komai karancin sa.

Maryam Garba ta kara da cewa saboda an wayi gari wahala ta sa mata da dama suna shiga munanan hanyoyi na zinace zinace don neman abin da za su samu su tallafi iyalan su saboda rashin da ake fama da shi a wannan lokaci ya sa mata da dama sun shiga mawuyacin hali wasu kuma sun kwashi cututtuka irin na zamani saboda neman abin da za su ci su tallafi iyalai, musamman wasu an mutu an bar su cikin wahala. Yayin da suma matasa a wannan lokaci rashin aikin yi da rashin ilmi ko mai tallafa musu wajen samun ilmi ya haifar musu da mutuwar zuciya da shiga cikin mawuyacin halin lalacewar tarbiyya inda daga bisani suke zama barazana ga tsaron kasa da mutanen kasa baki daya.


Advertisement
Click to comment

labarai