Connect with us

LABARAI

Ranar Dimokuradiyya: Saraki Ya Yi Gargadi Kan kokarin Kawo Wa Harkokin Siyasa Tarnaki

Published

on


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya janyo hankulan ‘yan Nijeriya da su guji yin ayyuka ko zantukan da za su iya sanya wa tsarin siyasar kasarnan tarnaki.

Saraki ya yi wannan gargadin ne cikin sakon da ya aike wa ‘yan Nijeriya a ranar bikin Dimokuradiyya na 2018.

Cikin sakon na shi, wanda mashawarcinsa na musamman kan harkokin manema labarai, Yusuph Olaniyonu, ya shelanta, Saraki, ya shawarci mutane da su sanya ido sosai su kuma fallasa duk wani yunkuri da suka hango na yi wa Dimokuradiyya zagon kasa, da kuma abubuwan karya dokar kasa.

Ya ma shawarci ‘yan kasa da ka da su yi wasa da morewar da suke yi wa tsarin na Dimokuradiyya na tsawon shekaru 19.

Shugaban na Majaisar Dattawa, ya yi kira kan bin doka sau da kafa, raba iko daidai wadaida, baiwa Majalisu karfin ikonsu, ‘yantar da sashen shari’a da samar da ‘yancin kafafen yada labarai.

“Ya wajaba mu kiyaye tsarin mulkinmu. A yanzun da muke bikin ranar Dimokuradiyya a yau din  nan, ina taya al’ummarmu murna da cewa wannan tsarin gwamnatin ya fi kowanne kyawo ya zuwa yanzun.

“Sai dai, lamarin ya fi gaban shirya zabuka a zabi shugabanni. Dimokuradiyya tana nufin bin dokokin kasa ne sau da kafa, sabanin mulkin ci da karfi.

A cewar shi, “Wannan shi ya sanya, bikin ranar Dimokuradiyya ba zai kammala ba, ba tare da janyo hankali kan duk wadansu abubuwan da suke kishiyantar Dimokuradiyyan ba, a daidai wannan lokacin da kasarmu ke tunkarar babban zaben 2019.”


Advertisement
Click to comment

labarai