Connect with us

LABARAI

PDP Ta Dirar Wa Jawabin Buhari Na Ranar Dimokradiyya

Published

on


Jam’iyyar PDP ta kwatanta jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi a bikin ranar Dimokuradiyya a matsayin fankan fayau, yabon kai da karyan ayyukan da bai yi su ba, sannan kuma ba tare da ya yi magana a kan batutuwan da ke ci wa al’umman Nijeriya tuwo a kwarya ba.

Cikin sanarwar da babban Sakataren yada labaran Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, ya fitar a Abuja, ranar Talata, Jam’iyyar ta PDP ta yi nu ni da cewa, wannan shi ne jawabi mafi muni da Buhari ya taba yi tun bayan hawansa kujerar mulkin kasarnan a 2015.

A cewar babbar Jam’iyyar adawan, an kawata jawabin shugaban ne da wasu jerin ayyukan bogi wanda na kusa da shi suka tsara masa domin a karkatar da hankulan ‘yan Nijeriya daga yadda gwamnatin na shi ta gaza a kowane sashe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kadan din ‘Yan Nijeriyan da har suka tsaya sauraron jawabin na shi, duk sun yi takaicin hakan, Shugaban kasan ya kasa ya nu na tausayawa kan halin kunci fatara da talaucewan da milyoyin ‘yan Nijeriya suke ciki a karkashin mulkin na shi.

“A bisa zahirin gaskiya ma, ko da shedara guda babu a cikin jawabin na shi wanda ke nu na tausayawa da kokarin yin adalci ga wadanda suka fuskanci take masu hakki, tsarewa ba bisa ka’ida ba, cin zalun da kuma wadanda ‘yan ta’adda da sauran makasa suka karkashe su, a Jihohin, Benuwe, Taraba, Zamfara, Kaduna,Plateau, Borno, Kogi, Yobe da sauran sassan kasarnan.

“Sam Shugaban kasan bai ce komai ba a cikin jawabin na shi wajen bayar da tabbacin daina yi wa tsarin mulki karan tsaye, da kuma yi wa Majalisun tarayya hawan kawara da yake yi da kuma maganan take hakkin ‘yan kasa.

“Shugaban kuma bai ce uffan ba kan ‘yar banzan sata, magudi da cuwa-cuwan da ake tafkawa a cikin gwamnatin na shi, inda ake samun Shugabannin Jam’iyyar na shi ta APC da ‘yan koren su su na satar Naira triliyon 10, yawanci ma daga ma’aikatar da ke karkashin kulawar sa kai tsaye.

Sanarwar ta PDP ta ce, abin mamaki ne yadda na kusa da Shugaban kasan suka zabi su dora shi bisa tafiye-tafiyen son rai, da bayar da bayanan ayyukan bogi, murguda bayanan halin da tattalin arzikinmu yake, inda kuma ya karke da kara bata shaksiyyarsa da tuni ta gama dushewa.

“Wannan kuma shi ne dalilin da ya sanya tun da farko Jam’iyyar PDP ta shawarci Buharin da ka da ya damu da batun yi wa ‘yan Nijeriya wani jawabi a ranar ta Dimokuradiyya.

A cewar Jam’iyyar ta PDP, ‘Yan Nijeriya sun rigaya sun zartar da hukuncin wannan ita ce shekara ta karshe da Buhari da Jam’iyyarsa ta APC za su yi bukin na Dimokuradiyya yana Shugaban kasa.

 


Advertisement
Click to comment

labarai