Connect with us

LABARAI

Kungiyoyin Jama’a Sun Yi Gangami A Bauchi Don Tunawa Da Wandanda Aka Kashe

Published

on


Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na al’umma sun yi gangami don nuna alhini da tunawa da mutanen da suka rasa rayukan su ta hanyar kashe kashe da suke aukuwa a Nijeriya, inda suka yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro kan su sake dabara game da yadda ake gudanar da tsaron jama’ar kasa.

Gangamin wanda aka gudanar da shi ranar litinin da ta wuce ya kunshi kungiyoyi masu yawa na kare hakkin ‘yan adam da kungiyar ‘yan uwa musulmi da sauran su inda suka sanya bakaken kaya tare kuma da rike alluna masu dauke da kashedi ga gwamnati game da yadda rayukan jama’a ke salwanta, har da bayyana alkaluman mutanen da suka rasa rayukan su lokuta dabam dabam yayin rigingimu da suke aukuwa musamman a arewacin Nijeriya. Don haka suka yi shiru na mintina don nuna alhini da tuna wadanda suka rasa rayukan su. Bayan haka kungiyoyin sun zaga shataletalen kofar wunti da ke cikin garin Bauchi don ankarar da jama’a musamman shugabanni kan halin da ake ciki na yawan kashe mutane da a ke yi a Nijeriya.

Musa Bayi Mohammed shi ne shugaban kungiyar Academic Forum na Jihar Bauchi cikin jawabin sa ya bayyana cewa sun yi wannan gangami ne don ankarar da gwamnati game da duba abubuwan da ke faruwa na kashe kashe a kasar nan ya fara wuce gona da iri,  don haka kowane mutum ya zabi wannan gwamnati ce don ya rayu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali amma matsaloli sun dabai baye mutane kullum suna rasa rayukan su, musamman ganin yadda a kullum kisan yana sake daukar sabon salo. Ana kashe Fulani a kore shanun su ana kasha kabilu a ce Fulani suka kasha su ana kama mutane a nemi kudin fansa idan an rasa a kashe su da sauran muggan hanyoyi da mutane ke rasa rayukan su.

Don haka Musa Bayi ya bayyana cewa matukar gwamnati bata sanya adalci da jin kayin mutanen da ta ke mulka da nuna gaskiya ba, mutane ba za su rike hannu su zauna suna ganin ana kashe su ba dole wata rana su ne kare kan su ta hanyar daukar doka a hannu wajen mai da martani don kare kan su. Don haka ya kara da cewa duk wanda ke raye yana kaunar a kare masa rayuwar sa idan kuma an wulakanta masa rayuwa Allah zai kama shugabannin wannan zamani da irin abubuwan da suke faruwa tun daga duniya ba sai an je lahira ba.

Ukasha Hamza Rahama Kakakin majalisar matasan Arewa yace sun zo ne don ankarar da gwamnati game da halin da ake cikim game da zubar da jinin mutane don haka  ya bayyana cewa duk mutumin da ya zabi gwamnati ya yi ne don ya zauna lafiya, hatta wadanda ke kare jama’a wato jami’an tsaro suma idan sun rasu iyalan su na shiga cikin wahala don yadda gwamnati ke watsi da su bayan mazajen sun mutu a bakin aiki amma ba a damu a kyautata musu ba. Saboda haka suke son gwamnati ta nunka himmarta game da samar da zaman lafiya da kare hakkin mutane, don haka kungiyoyi ke fitowa don a jan hankulan kungiyoyi su fito a nunawa gwamnati gazawar ta game da wannan al’amari, idan ba an gyara kasar ba za a wayi gari zaman lafiya ya fi karfin kowa kamar yadda ke faruwa a wasu kasashe na duniya.

Ukasha Hamza ya bayyana cewa akwai kungiyoyi na jama’a da na kare hakkin dan adam masu yawa da suke son shiga wannan gangami amma saboda kasancewar ana cikin lokacin azumi shi ya sa suka gudanar da tsaiwar da wuri kuma suka takaita lokacin wasu basu samu zuwa sun shiga ba.

Kuma an yi gangamin ne daga kowace kungiya ta musulmi da kirista da kowace kabila ta Nijeriya saboda yadda kowane mutum ke fiskantar rashin tabbas ga rayuwa ba tare da nuna banbanci ba.

Grace Tabshan daga kungiyar Bauchi Human Right Network cikin jawabinta ta bayyana cewa suna son a kawo karshen  kashe kashe da ake yi ya tsaya haka a samu salama don idan an ci gaba da kashe kashe dole za a wayi gari wasu su bukaci warewa daga kasar da ba ta da zaman lafiya.

Saboda haka ne suka bayyana cewa suna son shugabanni su san da tsaiwar da suka yi a wannan lokaci don kowa ya san cewa kungiyoyin ‘yan uwan junane babu banbancin addini ko kabila cikin lamari shi yasa suka hadu waje guda.

Sylbester Yibis dan rajin kare hakkin bil’adama na Global Right ya bayyana cewa sun tsaya ne don su bayyana cewa kashe kashe da ake yi ya ishe su haka, suma wadanda suka mutu su san cewa ba a manta da su ba don haka suka fito don  tunawa da abubuwan da ke faruwa a kasar nan na zubar da jini bias son zuciya da sakacin gwamnati da na mutane. Don haka ya bayyana cewa abin ya fara wuce tunanin mutum saboda a kullum kashe kashen daukar sabon salo suke yi idan yau an kashe sama da goma a Benuwai gobe  sai a kashe sama da arba’in a Zamfara jimawa sai a koma Borno a kashe mutane da dama kullum haka lamarin ke tafiya.

Saboda haka suke ganin zara bata barin dami dole su tashi tsaye su kirayi shugabanni da jimi’an tsaro kan a sake dabarun samar da tsaro a Nijeriya don a zauna lafiya a daina kashe rayuka a banza, saboda zaman lafiya shi ne gaba da komai. Don haka Sylbester ya bayyana cewa sun gudanar da gangamin a jihohi da daman a Nijeriya har da Abuja don tausayawa rayukan da suka salwanta daga kowace kusurwa ta kasar nan tare da nuna rashin jin dadi game da yadda kullum lamarin ke sake sabon salo madadin a samu ci gaba amma kullum komawa baya harkokin tsaro ke yi.

 


Advertisement
Click to comment

labarai