Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Gwamnan Taraba Shekara 14 A Gidan Yari

Published

on


Mai shari’a Adebukola Banjoko na babban kotun tarayya na babban birnin tarayya dake gundumar Gudu a shari’ar da aka yi shekara 11 ana tafkawa da tsohon gwamna jihar Taraba Mista Jolly Nyame, wanda ake zargi da allubazarantar da kudaden gwamnati har Naira Biliyan 1.6. kotun  ta yanke masa hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara 14.

Maishari’a Banjoko ya samu tsohon gwamnan ne da laifi har guda 27 a cikin laifuka 41 da ake zarginsa.

Harabar kotun ya samu halartar ‘yan sanda masu binciken motocin dake kokarin shiga da fita kotun, masu tafiya a kafa ma sai an bincike su kafin a bar mutum ya shiga harabar kotun.

Shari’ar ta tsawaita ne sakamakon daukaka kara da Nyame ke yi inda yake kalubalantar hurumin kotun ci gaba da sauraron karar da kuma ingancin tuhumar da hukumar EFCC take yi masa tun a wata Yuli na shekarar 2007.

Shari’a ya samu karfin ci gaba ne a lokacin da kotun koli ta yi watsi da karar ta kuma tabbatar da tuhumar da ake yi masa a shekarar 2016.

Hukumar EFCC tana karar Nyame ne da tuhuma 41 da suka hada da zamba cikin aminci da sata da karbar cin hanci da rashawa da kuma karbar wasu kaddarori bay tare da wani lura ba.

Mai gabatar da karar, yana karfafa tuhumar Nyame da karkatar da kudaden gwamnatin jihar Taraba har Naira Biliyan 1.64 a lokacin yana matsayin Gwamna.

Ana kuma zargin cewa, zamba cikin amincin daya aikata ya sabawa sashi na 315 na dokan manyan laifuffuka ta “Criminal Code Act”.

Lauyoyin masu gabatar da kara karkashin jagorancin Mista Rotimi Jacobs (SAN) ya kamala gabatar dahujojinsa a ranar 22 ga watan Nuwamba na shekarar 2016, bayan daya kawo mutane 14 a matsayin shaidu. Shi kuwa Nyame, baya ga kare kansa da ya yi, ya kuma kawo karin shaidu 3.

Tsohon gwamnan ya shigo kotun ne da misalin karfe 9.20 na safe saye da kaftan mai rowan kasa da hula ‘yar Maiduguri.

Mai shari’ar ya shigo kotun ne a dai dai karfe 9.40 na safe, bayan daya saurari wani kara sai ya bukaci a gabatar da shari’ar Nyame a dai dai karfe 9.46 na safe.

Bayan an kira “Case” din ne, sai Nyame, ya tashi ya shiga akwatin wanda ake tuhuma, daga nan ne mai shari’ar ya fara karanta hukuncun nasa da misalin karfe 9.51 na safe.

 


Advertisement
Click to comment

labarai