Connect with us

LABARAI

Karancin Albashi Ba Zai Samu Ba Har Zuwa Satumba —Gwamnatin Tarayya

Published

on


Sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata da aka shirya za a fara amfani da shi a watan Satumba kamar yadda ministan kwadago Mista Chris Ngige ya yi alkawari, ba za a samu aiwatar da shi kamar yadda aka shirya tunda farko.

An aiyana watan Satumba ne kwai don ya zama a lokacin aka kammala tattaunawa aka maganar mafi karancin albashin, inji Ngige, da yake zantawa da manema labarai a Abuja jiya.

Nigige ya kuma kara da cewa, “Kwamitin dake tattaunawa a kan mafi karancin albashin zai kammala aikinsa ne a karshen watan Satumba, daga nan zasu mika wa gwamnati rahoton nasu domin a kara tattaunawa da amincewa” daga nan kuma sai a tura rahoton zuwa majalisar jihohi daga nan kuma bangaren zaetaswa zai tura rahotona matsayin doka zuwa majalisar kasa domin amincewarsu.

Ya ce, akan haka ne kwamitin ya ziyarci sassan kasar nan domin tattaunawa da jama’a da kuma gwamnatocin jihohi da dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da kanfanoni masu zaman kansu.

A irin wannan zagayen ne wasu gwamnatocin jihohi suka gabatar da kudade daba daban a matsayin mafi karancin albashi, kudaden sun kai kamar Naira 22, 000 zuwa Naira 58, 000 daga abin da ake karba a halin yanzu na Naira 18,000.

A cewarsa, yawancin gwamnonin sun yi imanin cewa, in har ana son su iya aiwatar da mafi karancin albashi ne kawai in an sake fasalin tsarin raba arzikin kasa, sabaon fasalin kuma ya karawa gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi kudade daga asusun tarayya.

Ya ce, wasu jihohin kuma nada ra’ayin cewa, kada a kara albashi, a tsaya a kana bin da ake bayar wa a halin yanzu na Naira 18, 000, musamman gani har yanzu wasu jihohin ma basu iya biyan Naira 18,000 har yanzu maganan da ake ciki.

Daga nan ya kuma ce, duk da aikin kwamitin nada tsaurin gaske, amma dai ana samun ci gaba yadda ya kamata, ana son kuma a tafi da kowa da kowa, a saboda haka ne kuma aka sanya gwamnoni 6 a cikin kwamitin da kuma wakilcin kanfanoni masu zaman kansu.

A kan barazanar da kungiyoyin kwadago da jami’o’i suke yi na ci gaba da yajin aikin da suka dakatar saboda gwamnati bata cika musu alkawarin da tayi musu, Ministan ya kuma ce, a halin yanzun gwamnati na neman Miliyan 6 ne da zata biya musu bukatunsu.

Ya ce, kashi 95 da alkawuran da ake takaddama a kai an sa hannu akan su ne tun kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya kama mulki a shekarar 2015.

Ya kuma ce, yawancin yarjennyar da gwamnatin baya ta sanya wa hannu ba abun da za a iya cimma bane saboda dimbin kudaden dake a ciki.

Daga nan ya yi kira ga ma’aikata lafiya dake yajin aiki dasu koma bakin aiki a dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa domin biyan bukatunsu.

 


Advertisement
Click to comment

labarai